Karin bayani: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga Buhari kan kisan Zabarmari

Karin bayani: Majalisar wakilai ta aika sammaci ga Buhari kan kisan Zabarmari

- Daga karshe majalisar wakilai ta aika sammaci ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya gurfana a gabanta kan kisan Zabarmari

- A yayin zaman majalisa a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, zauren majalisar wakilan ya kaure da hayaniya yayinda yan majalisar suka sha bamban kan lamarin

- Sai dai kuma, an bukaci Shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta baci a wasu yankunan kasar

Bayan an kai ruwa rana, majalisar wakilai ta aika sammaci ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kisan manoma 43 a garin Zabarmari da ke jihar Borno, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Yan majalisar sun yanke shawarar ne a ranar Talata yayinda suka aminta da wani jan hankali da Satomi Ahmed yayi na cewa hakan na da matukar muhimmanci.

Da fari mun ji cewa hatsaniya ya kaure a majalisar wakilai kan wani kudiri da aka gabatar na neman a gayyato Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya amsa tambayoyi a kan hauhawan rashin tsaro a kasar.

Yanzu Yanzu: Hatsaniya ya kaure a majalisa kan bukatar gayyatar Buhari
Yanzu Yanzu: Hatsaniya ya kaure a majalisa kan bukatar gayyatar Buhari Hoto: TVC
Asali: UGC

A yayin zaman majalisar a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, daya daga cikin yan majalisar ya gabatar da wata bukata na gayyatar shugaban kasar gaban majalisar dokokin tarayya.

Amma sai lamarin ya tunzura wasu yan kashenin Buhari, don haka sai rashin jituwa ya gibta a tsakani, TVC ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa har yanzu Buhari ke ajiye shugabannin tsaro, Garba Shehu

Amma dai, bukatar neman Shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta baci a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma ya samu karbuwa a wajen yan majalisar.

Daga nan sai shugabannin majalisar suka shiga wata ganawa domin yanke hukunci kan banbancin ra’ayi da aka samu game da bukatar.

A baya mun ji cewa, biyo bayan kisan manoma 43 a jihar Borno wanda yan Boko Haram suka yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sauya tsarin tsaro a Najeriya.

Dr. Ahmad Lawan ya yi kiran ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa domin yi wa gwamnati da mutanen Borno jaje kan mummunan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta bukaci Buhari ya sallami Buratai, Sadiqu Baba, dss

A cewar Lawan, tsarin da ake dashi a kasa baya aiki, inda ya kara da cewa gwamnati na bukatar samun sabbin manufofi da kuma ganin yadda tsarin tsaron zai inganta.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel