Tsohon gwamnan Cross River Duke ya ce mayakan Boko Haram na samun makamai daga jami’an tsaro
- Donald Duke ya shawarci gwamnatin Najeriya a kan ta dauki matakan da ya kamata yayinda kasar ke fuskantar matsaloli na tsaro
- Tsohon gwamnan na jihar Cross River, ya kuma shawarci FG da ta inganta jin dadin sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro
- Duke ya kuma yi zargin cewa mayakan Boko Haram na samun makamansu daga jami'an tsaro sannan ya bukaci gwamnati da ta yi bincike kan lamarin
Tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke ya yi zargin cewa mafi akasarin makaman yan ta’addan Boko Haram ana samun su ne daga jami’an tsaro.
PM News ta ruwaito cewa da yake magana a tashar Channels TV, Duke ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan ta binciki rundunar tsaro sannan ta fitar da bara gurbi.
Legit.ng ta tattaro cewa Duke na martani ne a kan kashe-kashen da aka yi a jihar Borno dama wanda ake yi a fadin kasar, ya ce dole a sauya tsarin tsaron kasar musamman ta bangaren makamai, matakan ilimi da horarwa, da kuma jin dadin jami’ai.
“Mayakan Boko Haram wadanda ke da alhakin aikata yawancin ta’asar da ke gudana, suna samun makamansu ne daga jami’an tsaro.
KU KARANTA KUMA: Martanin 'yan Najeriya a kan rahoton matsawa gwamna Bello ya nemi shugaban kasa a 2023
“Yawancin makaman da Boko Haram ke amfani da su suna fitowa ne daga ma’ajin makamanmu, akwai bukatar mu yi duba cikin lamarin. Menene dalilin da yasa muke siyarwa makiyanmu da makamai?” Duke ya tambaya.
Duke ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta karfafa wa sojoi da yan sanda a yankin kudu maso gabas gwiwa domin cimma nasarori.
Tsohon gwamnan ya ce: “Ina ganin sojoji a yankin kudu maso gabas basu da karfin gwiwa, gwamnati ta karfafa masu gwiwa.
“Sannan zuwa yanzu, akwai bukatar mu bunkasa wata dabara a kan garkuwa da mutane. Shin ana karfafawa yan sanda gwiwa yadda ya kamata? Ina kokwanto kan haka, kuma basu da isasshen makamai.”
KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC
A wani labarin, Kungiyar NAS ta tofa albarkacin bakinta a kan harin da aka kai a Zabarmari.
NAS ta ce wannan hari yana cikin mafi muni da aka tani gani daga Boko Haram.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng