Fitacciyar jaruman fim ta ce karenta ya fi mata kawayenta masu tarin yawa

Fitacciyar jaruman fim ta ce karenta ya fi mata kawayenta masu tarin yawa

- Wata jarumar fina-finan Nollywood mai suna Nancy Iheme, ta ce karenta ya fi mata kawayenta da dama daraja

- Jarumar ta wallafa hotonta, rungume da karen, wanda ta sanya wa suna Dre, inda ta bayyana darajar karenta a wurinta

- Wannan wallafar ta janyo cece-kuce, har wani mabiyinta yana cewa kamar ba Dre ne ya cinye mata takalmi kwanaki ba

Sananniyar jarumar fina-finan Nollywood, Iheme Nancy, ta nuna tsananin kaunarta ga karenta, inda ta nuna tsananin rikon amanarsa har ya zarce na wasu kawayenta.

A wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram a ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwamba, jarumar tace zata iya jure shirmen karenta fiye da na wasu kawayenta. A cewarta, karenta ya fi kawayenta da dama.

Ta ce, sai ta zabi karenta fiye da kawayenta da dama. Ta yi wallafar ne tare da hotonta rungume da karen a shafinta na kafar sada zumunta ta Instagram.

KU KARANTA: Bidiyon mugun dukan da sojoji suka yi wa budurwa a kan kin gaiashesu ya janyo cece-kuce

Fitacciyar jaruman fim ta ce karenta ya fi mata kawayenta masu tarin yawa
Fitacciyar jaruman fim ta ce karenta ya fi mata kawayenta masu tarin yawa. Hoto daga Ihemenancy
Source: Instagram

Wannan wallafar ta janyo cece-kuce, inda wasu suke caccakarta, wasu kuma suke ganin sam bata da wani laifi.

KU KARANTA: Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan

Wata ndumefule_lilian, cewa tayi "lallai kawaye sun cutar da ke, ina ga Dre ne ya maye gurbinsu."

Wata Kaimajennifer ta ce: "Kamar ba wannan karen ne kwanaki ya cinye miki takalmi ba."

A wani labari na daban, wasu masoya 2 'yan kasar Kenya sun gano cewa yaya da kanwa suke, ana saura 'yan kwanaki kadan shagalin bikin aurensu.

An umarci John Njoroge ya dakata da shirye-shiryen aurensa da Rose Wanjiku, (ba sunayensu na asali ba), bayan ya turo magabatansa, The Nation ta wallafa.

Al'amarin ya daga wa Njoroge hankali, bayan ya gano cewa ubansu daya da Wanjiku domin diya ce ita ga kishiyar mahaifiyarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel