Shugabannin ASUU za su yi zama a Abuja domin duba yiwuwar bude Jami’o’i

Shugabannin ASUU za su yi zama a Abuja domin duba yiwuwar bude Jami’o’i

- A yau Kungiyar ASUU zata zauna kan maganar janye yajin-aikin da suke yi

- Shugabannin ASUU zasu zauna an jima a Abuja da nufin su fitar da matsaya

- An shafe watanni kusan 8 ba a karatu a jami’o’i saboda yajin-aikin na ASUU

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a a Najeriya ta samu kanta a cikin rabuwar kai a sakamakon matsayar karshe da gwamnatin tarayya ta dauka.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa rassan kungiyar ASUU na kowane jami’a suna tattauna wa a kan su koma aiki ko kuma su cigaba da yaji.

Ana sa ran cewa a yau Juma’a ne shugabannin ASUU na kasa za su hadu a birnin tarayya Abuja, inda za su dauki mataki game da janye yajin-aikin.

KU KARANTA: Ba har abada muka cire ASUU daga IPPIS ba - Minista

Wasu bangarorin ASUU sun tsaya tsayin-daka a kan cewa dole sai gwamnatin tarayya ta cika duka bukatun da suka gabatar kafin a bude jami’o’in kasar.

A daidai wannan lokaci kuma wasu rassan kungiyar malaman suna ganin ba a yin bari a dauke duka.

Kungiyar ASUU ta jami’ar ABU Zaria ta amince a koma aiki tun da gwamnati amince da bukatunsu, daga ciki har da biyan alawus na N40bn.

Masu wannan ra’ayi suna ganin cewa sai gwamnati ta biya kudin sannan za su koma bakin-aiki.

KU KARANTA: Rikicin ASUU da Gwamnati: Za a yi wa Malaman Jami’an takwara

Shugabannin ASUU za su yi zama a Abuja domin duba yiwuwar bude Jami’o’i
Ministan kwadago Hoto: www.sunnewsonline.com
Source: UGC

Malaman jami’ar FUPRE da ke jihar Delta suna ganin sai gwamnati ta cika duka alkawuran da tayi, sannan ya kamata ASUU ta janye yajin-aikin na ta.

ASUU na jami’o’in Maiduguri da Yobe suna so gwamnati tayi hobbasa kafin a koma bakin-aiki. Malaman jami’ar UAM suna so a biya su duk albashinsu.

‘Ya ‘yan ASUU na jami’ar UNILORIN sn ce basu goyon bayan hawa IPPIS, UNIJOS ba ta fitar da matsaya ba tukuna, haka zalika shiyyar kungiyar ta Sokoto.

A dalilin rashin tsaro da ake fama da shi a Zaria, wasu ‘yan Majalisa daga jihar Kaduna Kaduna sun bukaci IGP, COAS, FG su tsare Jami’ar ABU da ake ji da ita.

Idan za ku iya tuna wa 'yan majalisar sun fada wa Gwamnati da jami'an tsaro su baza dakaru, sannan a kafa doguwar katanga domin a kare ran al'umma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel