Dole a kare Jami’o’i da sauran wurare daga hare-haren ‘Yan bindiga inji Majalisa
- ‘Yan Majalisan Kaduna sun yi magana game da rashin tsaro a yankin Zaria
- Majalisa ta bukaci a baza Jami’an tsaro, sannan a katange jami’ar ABU Zaria
- Garba Muhammad Datti ya kawo wannan kudiri a gaban Majalisar Tarayya
A ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2020, majalisar wakilan tarayya ta koka game da matslar rashin tsaro da yake kara yaduwa a yankunan kasar nan.
Jaridar Punch ta ce majalisa ta yi wannan magana ne a dalilin hare-haren da aka kai a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da wasu makarantu a kasar.
Majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayyya, ‘ba tare da bata lokaci ba’, ta kafa katanga da zata zagaye jami’ar ABU kamar yadda aka yi a wasu jami’o’i.
KU KARANTA: An yi garkuwa d diyar tsohon Shugaban Jami'ar ABU Zaria
Majalisar ta ce: “Akwai bukatar a hana ‘yan bindiga da sauran bata-gari shigowa cikin jami’ar.”
“Wannan majalisa tana kuma kira ga Sufeta Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ‘ba tare da wani jinkiri ba, ya kafa sansanin ‘yan sandan kwana-kwana a jami’ar, musamman a shiyyar Samaru, domin a tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin jama’a a ko da yaushe.”
"Wannan gida tana kuma kira ga shugaban hafsun sojojin kasa, Janar Tukur Buratai ba tare da bata-lokaci ba, ya kafa bataliyar sojoji a iyaka ya Kudu da jami’ar ABU, domin hana kutsowa ta wannan yanki, wanda yanzu lamari (na rashin tsaro) ya yi suna.”
Bayan haka, majalisar wakilan ta bukaci kwamitocinta na harkar ilmi da tsaro su hada-kai da IGP, hafsun sojoji da ma’aikatar ilmi domin aiwatar da abubuwan da aka fada.
KU KARANTA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami'ar ABU Zaria
‘Dan majalisa mai wakiltar Sabon-Gari, Hon. Garba Muhammad Datti ne ya gabatar da wannan kudiri a majalisa domin kare jami’ar daga miyagun ‘yan bindiga.
Sauran wadanda su ka amince da kudirin sun hada da: Tajudeen Abbas, Shehu Balarabe, Muktar Ladan da Ibrahim Hamza Muhammad, duk daga mazabun Kaduna.
A cikin 'yan kwanakin jami'ar ABU Zariya ta na fuskantar barazana bayan an sace wata malamar asibiti da kuma wani Farfesa a sashen koyar da aikin likitanci.
Bayan haka, masu garkuwa da mutane sun shiga makarantar Nuhu Bamalli, sun sace wani malami da yara biyu, an harbi wani Bawan Allah a dalilin harin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng