Chris Ngige ya ce Gwamnati za ta yi wa takwarar ASUU, CONUA rajista

Chris Ngige ya ce Gwamnati za ta yi wa takwarar ASUU, CONUA rajista

- Gwamnatin Tarayya ta yi zama da tawagar kungiyar CONUA a garin Abuja

- Ministan kwadago, Chris Ngige, ya nuna gwamnati za ta yi wa CONUA rajista

- CONUA ta na kokarin kishiyantar kungiyar ASUU da ta dade ta na yajin-aiki

Yayin da kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta ASUU ta ke yajin-aiki a Najeriya tun watan Maris, gwamnatin tarayya ta na shirin yi mata kishiya.

Ministan kwadago da samar da aikin-yi na kasa, Chris Ngige, ya kyankyasa wa mutnae wannan a lokacin da ya gana da kungiyar CONUA a Abuja.

A ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, 2020, Dr, Niyi Sunmonu ya jagoranci kungiyarsa ta CONUA, su ka zauna da Ministan a birnin tarayya.

KU KARANTA: Buhari zai gana da ASUU

Kungiyar CONUA ta na kunshe ne da malaman jami’o’in da su ke adawa da tafiyar ASUU. Gwamnati ta nuna za ta yi wa wannan kungiya rajista.

CONUA ta samu tarba mai kyau, Ngige ya ce gwamnati ta na damar zama da su ko da ba su da rajista. “Mun hadu da ku yau a karon farko a ma’aikata.”

“Kun yi abin da ya dace da kuka nemi ayi maku rajista, kuma wannan ma’aikata ta yi abin da ya kamata, na soma yi maku rajistar.” Inji Ministan kwadagon.

Ministan ya ke cewa: “Mu na duba batun rajistarku. Na kafa wani kwamiti da zai duba lamarin. Zan fada wa kwamitin ya yi maza ya kammala wannan aikin.”

KU KARANTA: Gwamnati za ta kai ASUU kotu

Chris Ngige ya ce Gwamnati za ta yi wa takwarar ASUU, CONUA rajista
Chris Ngige Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“Za mu ba su makonni hudu daga yau, su kawo mana rahoto.”

“Daga cikin aikinmu shi ne mu yi wa kungiyoyi rajista, ya na kuma cikin aikinmu, mu taimaka wa kungiyoyin da ba su aiki.” Ngige ya ke fada wa CONUA.

A na su bangare, shugaban CONUA, Sunomunu ya bayyana cewa su na samun karin mabiya a jami’o’i tun da aka kafa kungiyar a farkon shekarar 2018.

Dazu kun ji cewa malaman Jami’a a karkashin kungiyar ASUU, sun shiga bankado tulin boyayyun dukiyoyin Akawun Gwamnatin Tarayya, Ahmed Idris.

Kungiyar ASUU da ke faman yajin-aiki ta koma wasan tonon silili ne da Ahmed Idris.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel