Tsame ASUU daga IPPIS na wucin-gadi ne, ba dindin bane, Ngige
- Cire kungiyar ASUU daga IPPIS na wucin gadi ne, za a amince da tsarin UTAS na wani dan lokaci ne, cewar Ministan kwadago da ayyuka
- Chris Ngige ya ce wajibi ne malaman jami'o'in da basu riga sun shiga tsarin ba IPPIS ba, su shiga don a biya su albashinsu
- A cewarsa, kafin a amince da tsarin UTAS, sai an dauki lokaci wurin bin hanyoyin tantance tsarin har sai an tabbatar da ingancinsa
Gwamnatin tarayya ta ce amincewa da bukatar ASUU, a kan cireta daga tsarin IPPIS, na wucin gadi ne. Da zarar lokacin ya wuce, za a mayar da ita kan tsarin.
Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin taron daidaitawa da kungiyar, The Cable ta ruwaito.
Bayan an yi ta rikici da ita a kan amincewa da tsarin IPPIS wurin biyan malamai albashi a ranar Juma'a, Ngige ya bayyana yadda za a yarda da tsarin da ASUU ta gabatar na UTAS na wani lokaci.
KU KARANTA: Shugabancin kasan yankin Ibo a 2023: Babu gudu, babu ja da baya, Sanata Abaribe
"Ina ga ya kamata mu yi karin bayani a kan wannan al'amarin, saboda mutane da dama cewa suke yi mun bar tsarin IPPIS, wanda ba gaskiya bane.
"Abinda muka ce a wancan taron da ya gabata shine, za mu bai wa NITDA da ofishin mai bayar da shawara a kan harkokin tsaron yanar gizo na kasa damar tantance tsarin UTAS tukunna.
KU KARANTA: EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi
"Amma na wannan lokacin, wajibi ne sauran malaman da basu shiga tsarin IPPIS ba su shiga, don a biyasu albashinsu da ba a biya su ba a baya, sannan a biya su kudaden da gwamnati ya kamata ta biya su na tallafin COVID-19, tsakanin watan Fabrairu zuwa na Yuni," yace.
Ministan ya bayyana cewa, gwamnati ba ta yi watsi da IPPIS ba, har yanzu tana nan a kan bakanta.
"Wannan tsarin tsani ne tsakanin IPPIS DA MINPSI na wani lokaci," a cewarsa.
Don haka za a cigaba da amfani da tsarin IPPIS har lokacin da aka gama tantance tsarin UTAS, ala bar shi idan an amince da ingancinsa, sai a fara amfani dashi.
A wani labari na daban, wannan al'amarin yazo ne bayan bayyanar wata takarda, wacce tayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, mai tabbatar da janye yajin aikin kungiyar.
ASUU ta wallafa hotunan takardar, inda tace kada mutane su aminta da labarin, na bogi ne.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng