'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon shugaban ABU, sunyi awon gaba da diyarsa

'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon shugaban ABU, sunyi awon gaba da diyarsa

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari gidan tsohon shugaban jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria, Farfesa Abdullahi Mustapha sun yi awon gaba da diyarsa.

Da ya ke tabbatarwa Daily Trust afkuwar lamarin, Farfesa Mustapha ya ce 'yan bindigan sun tafi gidansa ne misalin karfe 11.20 na dare.

Ya ce, "Eh, da gaske ne. Sun harbe mai gadi guda daya. Ba mu san ko su wanene ba kuma ba su tuntube mu ba har yanzu."

'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon shugaban ABU, sunyi awon gaba da diyarsa
'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon shugaban ABU, sunyi awon gaba da diyarsa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya gasa yi mata ciki

Da aka tuntube shi domin samun karin bayani, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya ce zai tuntubi 'yan sandan da ke Zaria domin ya samu cikaken bayani.

PRNigeria ta ruwaito cewa mutane hudu aka sace yayin harin.

Majiyar ta yi ikirarin cewa wadanda aka sace a gidan tsohon shugaban jami'an da ke Hayin Malam a Zangon Shanu da ke Zaria a jihar Kaduna sun hada da Maryam Abdullahi Mustapha, ma'aikaciyar ABU, yaran ta biyu da yayanta.

PRNigeria ta ce an ceti yaran biyu ne bayan daya daga cikin makwabta ya harbi daya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya kashe shi.

Masu garkuwa da mutanen sun sako yayan ne bayan sun gano cewa tana fama da ciwon asthma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel