Nuhu Bamalli Polytechnic: Injiniya Bello Atiku ya dawo gaban iyalinsa
- ‘Yan bindiga sun shiga gidajen ma’aikatan Nuhu Bamalli Polytechnic
- A sanadiyyar haka aka sace wani Malamin Makaranta da yara a Zaria
- Bayan kwanaki, miyagu sun fito da wadannan Bayin Allah dake tsare
A watan Nuwamban nan ne wasu ‘yan bindiga su ka shiga makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic, su ka yi gaba da wasu Bayin Allah.
Wani malamin makarantar, Bello Atiku ya na cikin wadanda aka tsere da su, aka yi garkuwa da shi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Injiniya Bello Atiku ya samu ‘yanci daga hannun wadannan miyagu, har ya dawo gaban iyalinsa.
KU KARANTA: 'Yan bindiga na yawo da jerin sunayen mutanen da za a dauke
Bello Atiku shi ne shugaban sashen fasahar ilmin na’ura mai kwakwalwa a tsangayar fasaha ta wannan makaranta ta koyon sanin aiki.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, 2020, cewa an saki Atiku tare da sauran wadanda aka sace.
An yi garkuwa da malamin makarantar gaba da sakandaren ne tare da wasu ‘ya ‘yan makwabtansa biyu.
Idan za ku iya tuna wa, an harbi iyayen wadannan yara, Malam Sanusi Hassan kafin a dauke yaran a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2020.
KU KARANTA: Miyagu sun je gida sun yi awon gaba da Malami a Jami'ar ABU Zaria
Mahaifin wadannan Bayin Allah, Sanusi Hassan, ma’aikaci ne da ke zaune a gidan ma’aikatan Nuhu Bamali Polytechnic da ke Zaria.
Mai magana da yawun bakin makarantar, Abdallah Shehu ya tabbatar da cewa mutanen nasu sun fito, ya ce za a fitar da jawabi daga baya.
Masu garkuwa da mutane a yankin Lokoja sun sun shiga hannu inda mutanen Gari su ka yi kukan kura su ka kama masu addabarsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng