‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mutumin kasar China a Jihar Taraba

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mutumin kasar China a Jihar Taraba

- Ana zargin masu garkuwa da mutane sun sace wani Basinne a jihar Taraba

- Miyagu sun dauke wani Ma’aikacin kasar Sin da direbansa a hanyar Wukari

- Wadannan ‘Yan bindiga ba su bukaci karbar kudin fansa ba har zuwa yanzu

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne, sun sace wani kwararren ma’aikaci da ke aiki a Najeriya daga kasar Sin.

Daily Trust ta ce wadannan miyagu sun sace mutumin kasar Sin din ne tare da wani direbansa a kan hanyar Donga zuwa garin Wukari, jihar Taraba.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, ‘yan bindigan sun tare titin ne, daga nan suka dauke Basinen da direbansa ba tare da jami’an tsaro sun yi komai ba.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sake yin barna a Zamfara

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadannan Bayin Allah suna cikin mota kirar Jeep lokacin da wadanda ake zargin masu garkuwan suka kama su.

‘Yan bindigan sun tuntubi wurin aikin mutumin a garin Donga, suka sanar dasu cewa sun tsare ma’aikacinsu tare da kuma wanda yake tuka motarsa.

Miyagun sun tabbatar da cewa mutanen biyu suna nan garau cikin koshin lafiya, amma har zuwa yanzu haka, ba su bukaci a biya kudin fansa ba tukuna.

Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma bai iya cewa komai ba a lokacin da ‘yan jarida suka tuntube shi.

KU KARANTA: An kama mata da 'danta dauke da wiwi

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mutumin kasar China a Jihar Taraba
Gwamnan Jihar Taraba Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jama’a sun kaurace wa titunan Donga da Takum a yankin Kudancin jihar Taraba, a dalilin ta’adin da ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane suke yi.

A kwanakin baya ne ma aka samu mutane suna bin wadannan hanyoyi, bayan abubuwa sun lafa.

A jiya ne mu ka ji cewa wani malamin jami'ar ABU Zaria ya aikawa Gwamna Nasir El-Rufai takarda mai ban tsoro game da rashin tsaron da ake fuskanta.

Yayin da ake fama da matsalar satar mutane, Gwamnati ta dage ne a kan karbar haraji a Kaduna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel