Malami ya rubutawa Gwamnan Kaduna budaddiyar wasika, ya ce babu zaman lafiya
- Wani Malami a Jami’ar ABU Zariya ya rubuta wasika zuwa ga Gwamnan Kaduna
- Muhammad Hashim Suleiman ya sanar da Gwamnati halin da mutanensa suke ciki
- A cewar Suleiman masu garkuwa da mutane sun dabaibaye yankuna, suna ta ta’adi
Muhammad Hashim Suleiman, wani malami a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya fito ya koka a kan halin rashin tsaron da duk al’ummar Zariya suke ciki.
Malam Muhammad Hashim Suleiman ya rubuta budaddiyar wasika ga mai girma gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai domin shaida masa halin da ake ciki.
Malamin da ke sashen koyar da ilmin yada labarai ya ce masu garkuwa da mutane sun yabaibaye yankunan Zaria kamar masu hakin ma’adanai sun samu gwal.
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun shiga gidan Sabo Nanono sun sace mutum daya
Wasikar ta ce: “Su na satar mutanen Zariya; mata da yara, wasu daga ciki ba a sanar da Duniya.”
Ya ce: “Shin ko ka san cewa bayan gonakin Shika sun gagari kowa shiga? Kana da labari cewa wurare irinsu Saye sun kama hanyar zama tamkar wasu kufai?
“Ka san cewa makiyaya dake wadannan yankunan sun tsere sun koma irinsu Kabama, Hayin Bagadaza dsr. cikin matsananciyar wahala.” Inji M.H Sulaiman.
Wasikar ta cigaba da sanar da mai girma gwamna: “Ka san wadannan masu garkuwa da mutane za su iya shiga cikin jami’armu cikin sauki, su dauke ma’aikata?
KU KARANTA: Dalibai sun huro wuta a bude Makarantun Jami’o’i
A cewarsa, wadanda suka fada hannun miyagun suna samun ‘yanci ne bayan sun saida filaye, gidaje ko motocin da suka dade suna wahala kafin su mallaka.
“Wadannan mutane ne za a taso gaba har da jami’an DSS a kan su biya ‘haraji’? Ka san har yau gwamnatinka ba ta fito ta yi wa ‘Yan Zariya wata magana ba.”
A wasikar ta sa, Muhammad Hashim Suleiman ya ba gwamnan Kaduna shawarar ya fito ya yi wa jama’a bayani tare da ba su kwarin gwiwar tsare dukiya da ransu.
A makon da ya wuce kuka ji cewa Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun sace wasu ɗaliban Jami'ar ABU a hanyar Kaduna-Abuja.
Ɗaliban suna kan hanyarsu ta zuwa Legas ne don samun horaswa a wata cibiyar koyon harshen Faransanci. Daga baya an biya kudin fansa, an saki daliban.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng