An kama uwa da ɗanta da kawu da sinƙin wiwi 49 a Kano

An kama uwa da ɗanta da kawu da sinƙin wiwi 49 a Kano

- Jamian 'yan sanda sun kama wani matashi da mahaifiyarsa da kawunsa kan zargin safarar tabar wiwi a Kano

- Matashin mai shekaru 21 ya bayyana cewa sana'ar mahaifinsa ne sayar da wiwi kuma mahaifyarsa ta umurci ya kawar da wiwin bayan an kama mahaifin

- Sai dai dubunsa ta cika a yayin da ya tafi gidan abokinsa don boye buhunnan wiwin amma jami'an tsaro suka damke shi

Wani matashi ɗan shekara 21, Kabir Mahmud ya shiga komar yan sanda bayan an kama da wani ganye da ake zargin tabar "wee-wee" ne.

Jaridar Vanguard ta ruwaito mahaifiyar Kabir, da kawunsa da wani da abokinsa suma sun shiga komar hukuma saboda alaka da tabar.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da faruwar lamarin bayan sun samu rahoton sirri da yake nuna an ga Kabir da buhun wiwi kuma an kama shi a unguwar Danbare da ke jihar.

An kama uwa da ɗanta da kawu da sinƙin wiwi 49 a Kano
An kama uwa da ɗanta da kawu da sinƙin wiwi 49 a Kano. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

An kama Kabir ne lokacin da ya ɗauko tabar zuwa gidansu a unguwar Gadonkaya daga inda ya ɓoye a Danbare wajen abokinsa.

Da ya aka matsa masa, ya yi ikirarin cewa wiwin mahaifinsa wanda yake hannun yan sanda, kuma ya na aiki ne bisa umarnin mahaifiyarsa wadda ta umarci da ya dauki tabar wiwin ya kai ta inda zai boye saboda kada ta zama hujja lokacin da yan sanda ke bincike a gidansu.

Kabir ya kuma ce kawunsa ne ya taimaka masa ya sama masa baburi ɗin adaidaitan da ya ɗauki tabar zuwa maboya.

A cewar sa, "ina shiryawa zan tafi wajen aiki sai mahaifiyata ta kira ni ta ke faɗa min yan sanda sun kama babana. Saboda haka inyi sauri in ɗauke wiwin daga gidan mu saboda ta na tsammanin yan sanda zasu zo bincike gidan.

KU KARANTA: Diego Maradona ya mutu yana da shekaru 60 a duniya

"Sai kawu na ya taimaka. Shi ya kira min babur don ɗaukar kayan.

"Sai na kira aboki na da ke Danbare na shaida masa zan zo in boye wiwin a ɗakinsa, kuma ya amince.

"Ina gidan kuma ban kai ga sauke wiwin ba jami'an anti-daba suka kama ni.

"Babana yana safarar miyagun kwayoyi ne sama da shekara 20. Ni ma gado nayi," Kabiru ya fadawa 'yan sanda.

Kakakin 'yan sandan, Haruna kiyawa, ya ce tuni Kwamishinan yan sandan jihar CP Habu Sani ya yi umarni a maida batun ga sashen binciken manyan laifuka CID don fadada bincike kan yadda aka shigo da wiwin Kano sannan a tafi kotu bayan kammala bincike.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel