Yan bindiga sun afka wasu kauyukan uku a Zamfara, sun kashe uku, mazauna gari sun tsere
- Yan bindiga sun kai hari kauyukan Magami, Tungar Haya da Sabon Sara a Jihar Zamfara
- Sun halaka mutane guda uku tare da kone gidaje da kuma sace kayan abinci da na masarufi
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da harin inda ta ce ramuwar gayya ne kan kashe wasu makiyaya uku
'Yan bindiga sun sake kai hari kauyuka uku a karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara, tare da kashe mutane biyu da tilastawa mazauna yankin hijira.
Kauyukan da abin ya shafa sune Magami, Tungar Haya da Sabon Sara kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Wani mazaunin yankin, Ibrahim Magami ya ce yan bindigar sun dira kauyukan a babura ranar Talata.
DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Ya ce sun zo kauyen Magami, suna harbi kan mai uwa da wabi har suka kashe mutum daya yayin da wasu suka gudu jeji don tsira da rayukansu.
Ya ce lokacin da yan bindigar su ka fuskanci babu kowa a cikin kauyen, sai suka balle shaguna suka kwashi kayan abinci.
Ibrahim ya ce, "yan bindigar sun kuma tafi Sabon Sara suka kuma kaddamar da irin wannan hari, inda nan ma suka kashe mutum daya kuma suka saci kayan abinci."
KU KARANTA: An kama uwa da ɗanta da kawu da sinƙin wiwi 49 a Kano
"Sun kuma kai hari Tungar Haya, suka kashe mutum daya tare da kunnawa kauyen wuta."
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce an kai hari kauyuka biyu, Magami da Tungar Haya, ya kara da cewa sun kashe mutane uku.
Ya ce, "harin ya faru ne sakamakon wani hari da aka kaiwa Fulani makiyaya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3 daga cikin su wanda yansakai suka kashe."
Ya kara da cewa an kai jami'an yan sanda don saita al'amura.
A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng