Zan kwace mulki hannun Gwamna Fintiri a 2023, Sanata Ishaku Abbo
- Sanatan da ya fita daga PDP ya bayyana ainihin dalilin da yasa ya koma APC
- A hirarsa da yan jarida, ya ce gwamnan bai fi karfinsa ba, kawai korarsa yayi
Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Ishaku Elisha Abbo, ya bayyana cewa ya sauya daga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) domin yayi takara a zaben gwamnan 2023.
Sanatan ya bayyana cewa zai kayar da gwamna Ahmadu Fintiri a zaben jihar a 2023, Daily Trust.
Yayin hira da manema labarai ranar Laraba a majalisa, ya ce duk da cewa yayi yaki tukuru domin ganin Fintiri ya yi nasara a zaben 2019, gwamnan ya koreshi daga PDP bisa rashin iya mulkinsa kuma ya kawo rabuwan kai cikiin jam'iyyar.
"Gwamnan bai kayar da ni ba. Kora ta gwamnan yayi (daga PDP). Na fita ne kawai domin in kwace kujerar daga hannunsa," Sanata Abbo yace.
KU KARANTA: Majalisar dattawa za ta gayyaci Pantami a kan hauhawar rashin tsaro
KU KARANTA: DHQ ta kaddamar da manhajar AFNDSP domin sojoji da iyalansu
Legit ta kawo muku cewa Sanata mai wakiltan Adamawa ta Arewa, Elisha Ishaku Abbo, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, zuwa masu rinjaye All Progressives Congress, APC.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana sauya shekan Abbo a wasikar da ya karanta ranar Laraba a zauren majalisa.
A wasikar, Sanata Abbo ya yi bayanin cewa ya yanke shawaran sauya sheka daga PDP be saboda salon mulkin gwamnan jihar Adamawa, Umaru Ahmed Fintiri.
Uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi watsi da labarin sauya shekar Sanata Ishaku Elisha Abbo zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, APC.
Uwar jam'iyyar PDP ta gargadeshi cewa ya sani za ta shigar da shi kotu kan hakan kuma bai isa ya tafi da kujerarta ba.
Da sauya shekarsa, yanzu APC na da Sanatoci 60, yayinda PDP na da 42.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng