Ministoci sun bayyana abin da ya sa aikin Abuja zuwa Kano yake cin lokaci

Ministoci sun bayyana abin da ya sa aikin Abuja zuwa Kano yake cin lokaci

- Gwamnan Kano yana kokarin ganin an gama aikin Abuja-Kaduna-Kano

- Ministoci, Hadimai da Gwamnoni sun yi zama da Julius Berger a Kaduna

- Ana sa rai cewa za a gama wannan aiki kafin Shugaba Buhari ya bar mulki

Ganin yadda aikin ginin titin Abuja zuwa Kano ya ke tafiyar hawainiya, gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi yadda za ayi aikin da wuri.

Shugaban kamfanin Julius Berger Nigeria Plc., Dr. Lars Richter, yayi bayanin halin da aikin yake ciki, da aka yi wani taro da al’umma a jihar Kaduna.

Wadanda suka halarci taron da aka yi sun hada da Ibrahim Gambari, Babatunde Raji Fashola, Zainab Shamsuna Ahmed da kuma Abdullahi Ganduje.

KU KARANTA: An dace a neman rijiyoyin danyen man fetur a Gombe – Gwamnatin Buhari

Julius Berger ya bayyana abin da yake daukar lokaci a wannan aiki daga canza tsari, zuwa yin hanyoyin ruwa da rage asarar ‘yan kasuwa da ke titin.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kudiri ganin an kammala wannan aiki na Abuja zuwa Kano.

Raji Fashola yake cewa dole aka canza aikin hanyar, aka kara fadin titin da kuma gadoji 40, don haka sai da gwamnati ta sake hayar wanda zai fito da tsarin.

Ya ce: “Kowane fadin hanya kilomita 375 ne. Idan ka nunka hudu, za ka samu muna yin titi mai kilomita 1500 ne." Duk kokarinka, Ministan yace za a ci lokaci.

KU KARANTA: Malami ya rubutawa El-Rufai budaddiyar wasika, ya ce babu zaman lafiya

Ministoci sun bayyana abin da ya sa aikin Abuja zuwa Kano yake cin lokaci
Titin Abuja zuwa Kano Hoto: JuliusBergerNigeria
Asali: Facebook

Ministar tattalin arziki da kasafin kudi, Zainab Ahmed, ta ce ko da yake a 2025 aka tsara za a kammala aikin, za suyi kokarin ganin an kare kafin nan.

Shamsuna ta ce: “Gwamnatin tarayya za tayi kokarin ganin ta karkare, an kaddamar da wannan aiki ga ‘yan kasa domin suyi amfani da shi a mulkin Buhari.”

Abdullahi Ganduje ya yi jawabi a taron da Ibrahim Gambari ya wakilci Mai girma shugaban kasa. Dr. Hadiza Balarabe ta gabatar da jawabin karshe, aka watse.

A jiya kun ji cewa Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya yi kaca-kaca da Majalisar Ingila kan zargin gwamnati da cin zarafin ‘Yan zanga-zanga.

Alhaji Lai Mohammed ya ce zargin an ci zararfin masu zanga-zangar #EndSARS, ba gaskiya bane.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel