Lai Mohammed ya ce hujjojin bogi ke nuna cin zarafin masu zanga-zangar EndSARS

Lai Mohammed ya ce hujjojin bogi ke nuna cin zarafin masu zanga-zangar EndSARS

- Najeriya ta yi martani game da barazanar da Majalisar Ingila ta ke yi mata

- Gwamnatin Tarayya ta ce hujjojin da Majalisar tayi aiki dasu duk na bogi ne

- Lai Mohammed yace wannan ya sha banbam da matsayar gwamnatin Ingila

Gwamnatin tarayya ta yi magana bayan samun labarin cewa ‘yan majalisar Birtaniya suna gudanar da bincike a kanta da jami’an tsaron kasar.

Ministan yada labarai na kasa, Lai Mohammed ya yi magana a madadin gwamnatin Najeriya, ya ce sam barazanar ‘yan majalisar Ingila ba ta damunsu.

Ministan ya shaida wa jaridar This Day a jiya cewa Birtaniya ba za ta iya maka wa gwamnatin Najeriya da jami’an tsaro takunkumi da rahoton bogi ba.

KU KARANTA: Ministan Ingila ya zargi Gowon da tafka mahaukaciyar sata

Alhaji Lai Mohammed ya yi martani ne game da rahoton da yake yawo na cewa an kai korafin jami’an tsaron Najeriya wajen ‘yan majalisar Birtaniya.

Mohammed ya ce majalisar ta kasar Birtaniya ta saki layi da ainihin gwamnatin kasar, wanda yace ba ta dauki ra’ayin da aka cusa wa ‘yan majalisar ba.

“Babu gwamnati mai hankali da za ta dogara da labarin bogi, ta sa wa gwamnati takunkumi, ba tare da ta tuntubi gwamnatinba.” A cewar Lai Mohammed.

A gefe guda, kuniyoyin Afenifere da Pan Niger Delta Forum (PANDEF) sun yaba wa ‘yan majalisar a kan binciken jami'an gwamnatin Najeriya da suka fara yi.

KU KARANTA: Alkali ya sa a kama Malamin Jami’a bisa laifin tafka magudi a zabe

Lai Mohammed ya ce hujjojin bogi ke nuna cin zarafin masu zanga-zangar EndSARS
Zauren Majalisar Birtaniya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ita kuwa kungiyar Arewa Consultative Forum ta nuna ba ta goyon bayan aikin ‘yan majalisar.

Mohammed ya ke cewa ‘yan majalisa ba za su iya hukunta wata kasa ba, sai dai su ba gwamnati shawara. A jawabinsa, ya yi watsi da rahoton da CNN ta yi.

Jiya kun ji ‘yan majalisar sun yi zama a kan zargin da ake yi wa mahukuntan Najeriya na cin zarafin wadanda su ka yi zanga-zangar lumanar #EndSARS.

Wata tsohuwar ministar Ingilar ta ba 'yan majalisar shawarar su sa kafar wando-daya da Najeriya

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel