Gwamnonin APC 3 da kan iya gadar Buhari a 2023

Gwamnonin APC 3 da kan iya gadar Buhari a 2023

A yayin da har yanzu ba a cika shekara da fara zango na biyu na mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba, tuni an fara mayar da hankali a kan waye zai maye gurbin Buhari a shekarar 2023.

Masu nazarin siyasar Najeriya sun yi tsokaci tare da yin hasashen cewa wasu gwamnoni kan iya samun nasarar maye gurbin Buhari a zabe na gaba.

Ga gwamnoni uku da suka zayyana da kuma dalilin da suka bayar.

1. Malam Nasir El-Rufa'i (Gwamnan jihar Kaduna): Tuni wasu kungiyoyin matasa sun fara bude ofisoshin yakin neman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Ana zargin cewa El-Rufa'i yana son arewa ta kara yin takarar shugaban kasa a 2023 saboda yana son samun tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC.

2. Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Gwamnan jihar Kano): Duk da ba kasafai ake saka shi a cikin 'yan siyasar arewa maso son kujerar shugaban kasa ba, akwai masu ra'ayin cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kan iya samun tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a shekarar 2023.

Masu wannan ra'ayi sun bayyana cewa, siyasar Najeriya na da sarkakiya. Sun fadi hakan ne saboda sanin cewa akwai wasu faya-fayan bidiyo da aka wallafa a wata jarida, inda a cikinsu ake zargin gwamna Ganduje ne ke karbar cin hanci.

Amma duk da hakan, masu ra'ayin Ganduje zai iya samun takara, suna kafa hujja ne da biyayya da kaunar da Ganduje ke yi wa Buhari. A ganinsu, Buhari zai so ya mika takara ga wanda zai kasance mai biyayya gare shi kuma dattijo.

Sannan suna kara kafa hujja da cewa Ganduje ya bawa Buhari da APC babbar gudunmawa a nasarar da suka samu a zaben 2019, a saboda haka za a iya bashi tikitin takara domin a yi masa sakayya.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe 'dagatai' 2 da shugaban 'Yansakai a jihar Taraba

3 Kayeode Fayemi (Gwamnan jihar Ekiti): Shine shugaban zauren gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti. Tsohon ministan an zabesa ne a matsayin shugaban gwamnonin Najeriya karkashin kakkarfan mulkin shugaba Buhari. Ya gaji Gwamna Abdulaziz yari na jihar Zamfara.

Wasu masu kiyasi a fannin siyasar sun yadda cewa, zata iya yuwuwa Fayemi ne mutumin da arewa zata ba goyon baya don maye gurbin burin da Asiwaju Bola Tinubu. Arewa na gani cewa, tsohon gwamnan jihar legas din zai iya zama barazana garesu wajen kwace ikon kasar nan. A don haka ne zasu iya amincewa da wanda bai kai shi buri ba kamar Fayemi a maimakon Jagaban siyasar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel