Myung-hee ta janye takara, Ngozi Okonjo-Iweala za ta lashe zabe babu hamayya
- Akwai yiwuwar Yoo Myung-hee ta janye kanta daga takarar kujerar WTO
- Wannan zai bada dama ga Ngozi Okonjo-Iweala ta yi nasara babu hamayya
- Lamarin yana neman canzawa bayan Donald Trump ya fadi zaben Amurka
Tsohuwar ministar tattalin arzikin Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta na iya karewa a matsayin tilon ‘yar takara a zaben shugaban kungiyar WTO.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2020, cewa akwai yiwuwar Misis Yoo Myung-hee ta janye takarar da ta ke yi.
Rahotannin da ake samu daga jaridar Washington Trade Daily sun nuna cewa mutumiyar Koriyar, Yoo Myung-hee za ta hakura da neman kujerar.
KU KARANTA: Myung-hee ta san aiki, shiyasa mu ke goyon-bayanta - Amurka
Idan har Ministar Koriya ta kudu mai shekaru 53 a Duniya ta fita daga wannan takara, kofar zama shugabar WTO za ta bude ga Ngozi Okonjo-Iweala.
Myung-hee wanda ita ce Ministar kasuwancin kasar Koriya, ta sanar da Amurka cewa ta janye takara.
Majiyar @washtradedaily ta na cewa: “Koriya ta shirya janye takarar Ministar kasuwancinta, Yoo (Myung-hee) daga neman shugabancin WTO..."
“Wannan zai bada dama ga ‘yar Najeriyar nan Ngozi Okonjo-Iweala, ta zama mace kuma ‘yar Afrikar farko da za ta zama Darekta Janar na kungiyar.”
KU KARANTA: Ngozi Okonjo-Iweala ta na sa ran nasara a zaben WTO
Wannan gajeren jawabi ya fito ne a shafin @washtradedaily na Twitter a ranar Talata.
Janye takarar na zuwa ne bayan ta tabbata Okonjo-Iweala ta samu goyon bayan rinjayen kasashe, yayin da Donald Trump yake mara baya ga Myung-hee.
Ganin yadda Donald Trump yake adawa da lamarin, gwamnatin Najeriya ta sha alwashin tsaya wa Ngozi Okonjo-Iweala domin ganin ta hau kujerar WTO.
Najeriya ta ce ta na sa ran cewa ‘yar takararta ta zama shugabar kungiyar kasuwancin. Ma’aikatar harkokin kasasashen wajen Najeriya ta fadi haka.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng