Duk da haka, ina sa ran a ji alheri a zaben WTO Inji Ngozi Okonjo-Iweala
- Okonjo-Iweala ta ji dadin goyon bayan da kasashen Duniya su ka ba ta
- Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta nuna cewa ta na sa ran ta kawo kujerar WTO
- Amurka ba ta goyon bayan Okonjo-Iweala mai takardar zama ‘yar kasa
Tsohuwar ministar tattalin arzikin Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta ce ta na sa ran zama sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci ta WTO.
Ngozi Okonjo-Iweala wanda kafarta daya ta ke kan kujerar WTO ta ce duk da je-ka-ka-dawon da ake samu a zaben da ta shiga, tana hango nasara.
Jaridar Punch ta ce Okonjo-Iweala wanda ta rike har darekta a babban bankin Duniya ta ji dadin yadda kasashen Duniya su ka ba ta goyon-baya.
KU KARANTA: Meyasa Amurka ta ke yi wa Dr. Okonjo-Iweala adawa gar-da-gar?
Dr. Okonjo-Iweala ta bayyana wannan ne a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, 2020.
“Ina farin cikin nasara da cigaban da na samu a takarar shugabancin @WTO. Kai na a kasa, da aka bayyana ni a matsayin wanda ta fi kuri’a tsakanin ‘ya ‘yan kungiya, kuma wanda ta fi yiwuwar samun mubaya’a.”
Okonjo-Iweala ta cigaba da cewa: “Za mu tafi zuwa mataki na gaba a ranar 9 ga watan Nuwamba.”
Jawabin Ngozi Okonjo-Iweala shi ne na farko tun bayan da labari ya bayyana cewa ita ce ta ke kan gaba a kuri’ar da aka yi tsakanin kasashe 164 na kungiyar.
KU KARANTA: Kasashe 106 su na-bayan goyon tsohuwar Ministar kudin Najeriya
“Za mu cigaba da sa rai.” Inji mutumiyar Najeriya mai shekaru 66.
Kalubalen Okonjo-Iweala shi ne rashin goyon bayan Amurka, inda kasar ta ke tallata wanda ta rage a takarar wannan kujera, Yoo Myung-hee.
A lokacin da Okonjo-Iweala ta rike kujerar Darekta a bankin Duniya, sun zo da wasu tsare-tsare da ba dole ba ne su kwanta wa shugaban Amurka Donald Trump.
A baya gwamnatin Donald Trump ta nuna wa Akinwumi Adesina irin wannan adawa a AfDB.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng