Shugaban Amurka, Trump ya sanya wa kasashen Afrika 15 sabbin takunkuman shiga kasar
- Amurka ta kakaba wa wasu kasashen Afrika sabbin takunkumai na shiga kasarta
- A sabuwar dokar tafiye-tafiye na Shugaba Donald Trump, dole sai kasashen sun fara biyan dala 15 kafin amincewa su tafi kasar
- Sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Disamba
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wata sabuwar dokar tafiye-tafiye ga kasashen Afrika 15 inda za su biya dala 15,000 kafin su ziyarci kasar.
Wannan sabuwar doka da aka sanya za ta fara aiki ne a ranar 24 ga watan Disamba, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar, wannan shiri na wa’adin watanni shida wanda zai shafi masu ziyartar Amurka da yan kasuwa zai zamo darasi ga masu zama bayan bizarsu ta kare.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dokokin Ondo ta tsige mataimakin kakakinta Iroju Ogundeji
Trump, wanda ya sha kaye a zaben kasar da aka gudanar, ya mayar da tsaurara matakai na shige da fice abu mai matukar muhimmanci a lokacin wa'adin mulkinsa na shekara hudu.
Zababben shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden ya dau alkawarin sauya wasu matakan da Trump ya dauka musamman kan shige da ficen kasar.
Sabon tsarin bizar zai shafi kasashen da kashi 10 cikin 100 na al’ummansu da ke zuwa Amurka su wuce iya lokacin da aka ba su na zama a shekarar 2019, kuma a yanzu za a nemi su biya wasu kudade kimanin dala 5,000 da dala 10,000 ko kuma dala 15,000.
Sai dai a yayin da yan wadannan kasashe ke wuce lokacin zamansu a Amurka, masu zuwa daga kasashen ba su da yawa, kamar yadda Reuters ya ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni
Kasashen da matakin ya shafa sun hada da:
1. Angola
2. Burkina Faso
3. Chadi
4. Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo
5. Djibouti
6. Eritrea
7. Gambia
8. Guinea-Bissau
9. Liberia
10. Mauritania
11. Sudan
12. Sao Tome
13. Cape Verde
14. Libya
15. Burundi
A wani labarin, mun ji cewa tohuwar ministar Birtaniya, Theresa Villiers ta yi kira ga gwamnatin Ingila ta maka takunkumi a kan jami’an gwamnatin tarayyar Najeriya.
Villiers ta ce bayanan da ta samu daga 'yan mazabarta wanda asalin ‘yan Najeriya ne ya nuna cewa an ci zarafin ‘yan zanga-zangar #EndSARS.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng