"Mu dauki mataki a kan wadanda su ka ci zarafin masu zanga-zanga a Najeriya"

"Mu dauki mataki a kan wadanda su ka ci zarafin masu zanga-zanga a Najeriya"

- Kasar Ingila ta tattauna zargin cin zarafin masu zanga-zangar #EndSARS

- Majalisar Ingila ta fara duba zargin da ake yi a kan jami'an tsaron Najeriya

- Wata tsohuwar Ministar Birtaniya ta na so a hukunta shugabannin kasar

Tsohuwar ministar Birtaniya, Theresa Villiers ta yi kira ga gwamnatin Ingila ta maka takunkumi a kan jami’an gwamnatin tarayyar Najeriya.

Theresa Villiers ta na so a hukunta gwamnatin Najeriyan ne a game da yadda ta dauki matakai masu tsauri a kan masu zanga-zangar lumana.

Villiers ta ce bayanan da ta samu daga 'yan mazabarta wanda asalin ‘yan Najeriya ne ya nuna cewa an ci zarafin ‘yan zanga-zangar #EndSARS.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta zauna da ASUU

Jagorar jam’iyyar mai mulki ta nemi gwamnatin Ingila ta sa takunkumin hana fita, sannan a rike dukiyoyin wadanda aka samu da laifin cin zarafi.

‘Yar siyasar ta gabatar da bukatarta ne a lokacin da aka shafe kusan sa’a guda da rabi ana muhawara game da lamarin #EndSARS a majalisa.

Wasu ‘yan majalisa masu-ci sun goyi bayan Theresa Villiers, sun nuna cewa ta haka na kawai gwamnatin Ingila za ta nuna wa Najeriya fushinta.

Daily Trust ta ce Birtaniya ta saurari koken mutanen Najeriyar ne bayan korafin da wani Siles Ojo ya fitar ya samu sa hannun mutane sama da 220, 000.

"Mu dauki mataki a kan wadanda su ka ci zarafin masu zanga-zanga a Najeriya"
Majalisar Ingila Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Majalisar adawa ba su goyon bayan Yakubu ya koma INEC

Wadanda su ka sa hannu a wannan korafi su na neman Birtaniya ta sa takunkumi a kan manyan Najeriya da jami’an ‘yan sanda dake wuce gona-da-iri.

‘Yan majalisan sun tafka muhawarar nan ne tsakanin karfe 7:00 zuwa 8:30 a daren ranar Litinin.

Idan mu ka dawo siyasar gida za mu ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan ya fada wa ’yan kasar suyi waje da su a 2023.

Dr. Ahmad Ibrahim Lawan da ya ke kare aikin majalisu, ya ce jama'a su kaurace wa 'yan majalisar idan zabe ya zo idan har sun gaji da ganin fuskokinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel