Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni

Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni

- Kotun gargajiya a Ibadan ta raba auren wasu ma'aurata da suka shafe shekaru goma tare har da 'ya'ya biyu

- Matar ce ta bukaci a ruguza auren bisa zargin mijinta da yunkurin tsafi da ita da kuma saduwa da ita na tsawon awanni

- Alkalin kotun ya wargaza aure domin ganin an samu kwanciyar hankali da zaman lafiya

Wata kotun gargajiya a Ibadan, a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, ta wargaza auren shekaru 10 tsakanin wata Basirat Adeyoyin da mijinta, Adeyoyin Niyi kan yunkurin kudin asiri da yawan saduwa.

Da yake zartar da hukunci, alkalin kotun, Cif Ademola Odunade ya bayyana cewa kotun ba za ta zuba idanu tana kallo har sai an samu rashin tsari ba kafin ta yanke hukunci.

Don haka Odunade ya rushe aure tsakanin ma’auratan don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, jaridar The Nation ta ruwaito.

Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni
Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Twitter

Ya mika ragamar kula da yaran da suka haifa su biyu a hannun mahaifiyarsu sannan ya umurci mijin ya dunga biyan N10,000 duk wata a matsayin kudin abincinsu.

KU KARANTA KUMA: 2023: Ku kunyata ni ta hanyar mikawa kudu maso gabas tikitin shugaban kasa, Umahi ga PDP

Kotun ta kuma umurci Niyu da ya dauki nauyin karatu da sauran jin dadinsu.

A bayananta na baya, Basirat, wacce ke zama a Olonsogo-Molete, ta fada ma kotun cewa tana neman a raba aurenta da mijinta saboda “yana kokarin amfani da ita don kudin asiri.”

Matar ta kara da cewa ta fara lura da hakan ne lokacin da mijin bai nuna kowani damuwa ba a yayinda ta yi barin cikinta na karshe saboda yawan saduwa da ita.

“Kawai a 2018, sai Niyi ya dawo gida wata rana da daddare sannan ya fada mani cewa ya samu sakon cewa dole sai ya shafe tsawon kwanaki bakwai yana tarayya dani ba tare da bayar da tazarar ko kwana daya ba.

“Ban damu da yiwa abun wani fassara ba sannan na kyale shi ya dungi tarawa dani har sai da aka samu matsala.

“Kafin wannan lokacin ina dauke da juna biyu na watanni uku sannan a rana ta biyu da fara saduwa ba kakkautawa, sai na yi barin cikin.

“Na kula da kaina a asibiti kawai sai ga Niyi ya dawo gida sannan ya fara neman mu ci gaba daga inda muka tsaya duk da cewar ina zubar jini.

“Sai na tuntubi iyayena da yan uwa kuma daga haka, sai muka gano cewa yana kokarin amfani dani ne don yin kudin asiri,” in ji Basirat.

Da yake amsa karar, wanda ake kara bai karyata zargin yawan saduwan ba amma ya kawo wani sabon batu.

Niyi ya bayyana cewa matarsa rigimammiya ce sannan cewa ta kasance mace mai sakaci.

KU KARANTA KUMA: Makashi ya fille wa mahaifi kai, ya halaka da har lahira a Kano

“Koda wannan kotu za ta raba auren, ina rokonta a kan ta bani ragamar kula da yaran biyu saboda Basirat ba za ta iya kula da su.

“Daya daga cikin matasan da ke makwabtaka da mu ya yiwa yarinyarmu ta farko fyade kuma bata fada mani faruwar lamarin ba.

“Ya mai shari’a, saboda yadda take dadewa a kasuwa ne irin wannan abun ya afku,” In ji Niyi.

A wani labarin, wani tsohon dan shekaru 72, Musa Abdullahi, ya bukaci wata kotu da ke yankin Gwagwalada, Abuja, da ta tursasa wata budurwa yar shekaru 18, Rukayya Idris, ta biya shi kudi N50,200 da ya kashe mata tunda ta ki yarda da tayin auren da yayi mata.

Abdullahi, wanda ke zama a Baure Anguwar Hausawa a Gwagwalada, ya fada ma kotu cewa ya nemi auren Rukayya a watan Yunin 2020 sannan ta amince za ta aure shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel