Yanzu Yanzu: Ku yi waje da mu idan kun gaji da ganin fuskokinmu, Lawan ga ‘yan Nigeria

Yanzu Yanzu: Ku yi waje da mu idan kun gaji da ganin fuskokinmu, Lawan ga ‘yan Nigeria

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci ’yan Najeriya da su yi waje da duk dan majalisar da bai yi musu ba a 2023

- Lawan ya soki masu kira da a soke majalisar dattawar saboda makudan kudaden da ake biyan sanatoci

- Ya ce soke majalisar za ta haifar da matsala na rashin tsari a kasar

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi gargadin cewa za a fada yanayi na rashin tsari idan har aka soke majalisar dattawa kamar yadda wasu ‘yan Najeriya suka bukata.

Maimakon haka, ya kalubalanci wadanda basu gamsu da sanatocin da ke majalisar ta tara ba da su yi waje da su a 2023 idan har sun san cewa basa son ganin fuskokinsu.

Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, yayinda yake kaddamar da bude taron ma’aikatan gudanarwar majalisar tarayya da na hukumar ayyukan majalisar a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Magidanci ya gudu ya bar matarsa da ‘yan uku da ta haifa saboda kudin asibiti

Yanzu Yanzu: Ku yi waje da mu idan kun gaji da ganin fuskokinmu, Lawan ga ‘yan Nigeria
Yanzu Yanzu: Ku yi waje da mu idan kun gaji da ganin fuskokinmu, Lawan ga ‘yan Nigeria Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

Ya bayyana majalisar dattawa a matsayin mai tabbatar da daidaito wajen ganin an wakilci dukkanin yankunan kasar sabanin majalisar wakilai inda jihohi da suka fi yawan al’umma suka fi samun yawan wakilai.

Shugaban majalisar dattawan ya kuma soki sharhin wadanda ke neman a soke majalisar dattawan saboda kaso mai tsoka da sanatocin suke karba, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce kasafin kudin majalisar dokokin tarayya ya kasance kasa da kaso daya cikin dari na kasafin kudin kasar na 2021.

KU KARANTA KUMA: Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera

A wani labarin, Gwamnatin Najeriya ta shiga sabuwar yarjejeniya da gwamnatin jamhurriyar Nijar na fara shigo da man fetur birnin Zinder.

The Nation ta ruwaito cewa Ministan arzikin man fetur na Najeriya, Temipre Sylva, da Ministan man jamhurriyar Nijar, Mr. Foumakoye Gado, ne suka rattafa hannu kan yarjejeniyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel