‘Yan PDP za su nemi su jawo wa tazarcen Mahmud Yakubu tasgaro a Majalisa

‘Yan PDP za su nemi su jawo wa tazarcen Mahmud Yakubu tasgaro a Majalisa

- ‘Yan majalisar adawa ba su goyon bayan Mahmud Yakubu ya sake rike INEC

- Sanatocin PDP suna ganin cewa sam bai dace Yakubu ya koma kan kujera ba

- Marasa rinjaye a Majalisar sun yi wani zama inda su ka tsara abin da za suyi

Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP a majalisar dattawa sun shirya domin hana a amince da sabon wa’adi ga Farfesa Mahmood Yakubu a hukumar INEC.

Jaridar This Day ta ce ‘yan adawan da ke majalisar tarayyar ba su goyon bayan Mahmood Yakubu ya sake shafe wasu shekaru biyar ya na rike da hukumar.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan majalisar tarayya sun dawo daga hutun da su ka je, yanzu an cigaba da sauraron zaman kare kasafin kudin shekarar badi.

KU KARANTA: Abin da ba a taba yi ba, Buhari ya zabi Yakubu ya cigaba da rike INEC

Majiya daga jaridar ta bayyana cewa sanatocin PDP sun hadu a karshen makon da ya gabata, sun amince cewa ba za su yarda da nadin Mahmood Yakubu ba.

A farkon watan nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuto takarda zuwa majalisa yana neman a sake ba Mahmood Yakubu wa’adi na biyu a INEC.

Sanatocin na PDP marasa rinjaye za su yi adawa da nadin Yakubu ne bisa la’akari da kwan gaba-kwan bayan da su ka ce ya rika yi a karon farko da ya yi a ofis.

‘Yan majalisar suna kuka a kan yadda INEC ta fito a 2019 ta ce ba tayi amfani da na’urar tattara sakamako ba, sai kuma aka ga labarin ya canza a zaben Edo/Ondo.

KU KARANTA: Ba za a samu duk takarduna da ake nema ba – Magu

‘Yan PDP za su nemi su jawo wa tazarcen Mahmud Yakubu tasgaro a Majalisa
Tsohon Shugaban INEC, Yakubu Hoto: gettyimages
Asali: Getty Images

Majiyar ta rahoto: “Mu a PDP ba za mu iya amince wa Yakubu ya cigaba da gudanar mana da zabe a kasar nan ba, mun yi imani ba za a taba yi mana adalci ba.”

“A kan haka, za mu yi adawa da sake zaben shi da shugaban kasa ya yi.” Inji Majiyar.

A farkon watan nan kun ji cewa tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya mika ragamar hukumar zabe na kasa ga shugaban rikon kwarya.

Wa'adin Yakubu ya kare ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, inda ya ke jiran a sabunta nadinsa bayan shugaban kasa ya sake zaben shi a wani karo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng