Kotun Akwa Ibom ta ce a kamo Farfesa Ignatius Uduk inji Lauyan INEC

Kotun Akwa Ibom ta ce a kamo Farfesa Ignatius Uduk inji Lauyan INEC

- Kotu ta bada umarnin a kamo mata Farfesa Ignatius Uduk a Akwa Ibom

- Hukumar INEC ta na zargin Ignatius Uduk da taba mata alkaluman zabe

- A baya an bukaci Farfesan na jami’ar Uyo ya bayyana gaban INEC, ya ki

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa babban kotun jihar Akwa Ibom da ke zama a garin Uyo, ya bada umarnin a cafke Farfesa Ignatius Uduk.

Alkalin ya bada wannan umarni ne kwanaki kadan bayan wani kotu da ke zama a garin Ikot- Ikpene, ya gurfanar da wani Farfesan, Peter Ogban.

Shi ma Ignatius Uduk wanda ya fito daga jami’a daya da Peter Ogba, hukumar zabe na kasa, INEC tana zarginsa da hannu a laifin magudin zabe a 2019.

KU KARANTA: Sanatocin PDP sun lashi takobin hana a amince da Yakubu a kujerar INEC

INEC ta na zargin Peter Ogban da taba sakamakon zaben da bai cikin wadanda su ka yi aikin tattara wa.

Hukumar mai zaman kanta ta fitar da jawabi ta bakin shugaban sashen wayar da kan jama’a game da sha’anin zabe, Odaro Aisien, game da shari’ar.

Odaro Aisien ya ce INEC ta yi kokarin zama da Farfesa Peter Ogban, amma abin ya faskara duk da an yi ta aika masa takardu ta jami’arsa ta UNIUYO.

Aisien ya ke cewa INEC ta tafi kotu bayan Farfesan ya yi watsi da takardar da aka rika aika masa.

KU KARANTA: 2023: Duk wanda ya iya allonsa ya wanke - Jigon APC

Kotun Akwa Ibom ta ce a kamo Farfesa Ignatius Uduk inji Lauyan INEC
Shugaban INEC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

A karshe Alkali ya duba bukatun INEC, ya bukaci wanda ake nema ya hallara gaban kuliya a ranar 18 ga watan Nuwamba, duk da haka ya ki zuwa kotu.

Ganin abin ya faskara, sai Lauyan hukumar INEC, Kpoobari Sigalo, ya roki kotu ta sa a cafke Ogban, Lauyan ya ce an kuma amince da wannan rokon.

Kun ji cewa ‘yan kwadago sun wulakanta wakilan gwamnatin tarayya a Aso Villa wajen taron da aka shirya a game da karin farashin man fetur da aka sake yi.

Kungiyoyin kwadago sun fasa zama da Ministoci, su ka zargi gwamnati da rashin fito da gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng