NLC da TUC sun fice daga dakin taro ana tattaunawa da Gwamnatin Tarayya

NLC da TUC sun fice daga dakin taro ana tattaunawa da Gwamnatin Tarayya

- A jiya ne aka shirya za a tattauna tsakanin Gwamnati da kungiyoyin kwadago

- Wannan zama bai yiwu ba, wakilan kungiyoyin NLC da TUC sun yi tafiyarsu

- Shugabannin kwadago su na zargin gwamnati da rashin gaskiya a lamarinta

Shugabannin kungiyoyin kwadago sun tashi sun yi tafiyarsu yayin da ake kokarin tattauna wa da Ministan kwadago da wakilan gwamnatin tarayya.

Jaridar Daily Trust ta ce shugabannin ma’aikatan kasar sun fice daga taron da ake yi a dalilin karin kudin man fetur da gwamnatin Najeriya ta sake yi.

‘Yan kwadagon sun bayyana cewa ba za su iya cigaba da zama a kan tebur da gwamnati ba, saboda surutun da su ke fuskanta daga wajen talakawa.

KU KARANTA: Za a tada tawagar musamman da za ta zauna da Shugabannin ASUU

Shugaban kungiyar TUC, Quadri Olaleye, ya ce shugabannin kwadago da-dama ba su halarci zaman ba saboda gwamnati ta na jefasu a cikin hadari.

Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, ya zargi gwamnatin tarayya da rashin fito masu a mutum. Ugboaja ya ce akwai yaudara a lamarin gwamnatin kasar.

“A tsawon lokaci, mun yi zama da-dama da gwamnati a kan karin mai da farashin wuta. Mun samu fahimta, amma ana kan zama, sai mu ka ji an lafta kari a kan farashin mai.” Inji Ugboaja.

Emmanuel Ugboaja ya ce su na ganin hakan ya ci karo da abin da su ka tattauna da gwamnati.

KU KARANTA: Tsohon Ministan ‘Yaradua, Kazaure ya zama Surukin Gwamna El-Rufai

NLC da TUC sun fice daga dakin taro ana tattaunawa da Gwamnatin Tarayya
FG za ta sake gayyatar NLC da TUC Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

A zaman da aka shirya ranar Lahadi, NLC ta dauka za a fara tabo batun karin kudin mai, sai ta ji ana wata magana dabam, a dalilin haka ta tashi, ta bar taron.

A cewar Ugboaja, ba a samu fahimta tsakaninsu da gwamnati a kan karin farashin man fetur ba. “Mu ka ga cewa ba za mu iya cigaba da zama da gwamnati. ba”

Wadanda su ke wajen taron da ‘yan kwadagon su ka tattara su ka yi tafiyarsu su ne: Chris Ngige, Festus Keyamo, Timiprye Sylva, Goddy Agba da Boss Mustapha.

A makon da ya gabata ne ku ka ji cewa malaman kami’a da ke kungiyar ASUU sun shiga bankado tulin boyayyun dukiyoyin Akawun Gwamnatin Tarayya.

Kungiyar ASUU ta koma wasan tonon silili da Ahmed Idris, ta ce ya na da kadarori a boye.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel