Yanzu yanzu: Farfesa Yakubu ya sauka daga kujerar shugaban INEC, yana jiran tsammani

Yanzu yanzu: Farfesa Yakubu ya sauka daga kujerar shugaban INEC, yana jiran tsammani

- Shugaban hukumar zabe ta kasa, INEC, Farfesa Yakubu Mahmoud ya sauka daga kujerarsa

- A yanzu yana jiran tsammani kafin majalisar dattawa ta sabonta mai nadin nasa a karo na biyu

- Ya mika ragamar shugabanci ga kwamishinan zabe na kasa, Air Vice Marshal Muazu Ahmed mai ritaya a matsayin shugaban rikon kwarya

Farfesa Mahmoud Yakubu ya sauka daga kujerarsa a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).

Ya mika ragamar shugabanci ga kwamishinan zabe na kasa, Air Vice Marshal Muazu Ahmed mai ritaya, a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba.

Hakan ya gudana ne a wajen wani taro da aka gudanar a hedkwatar hukumar zaben da ke Abuja, babbar birnin tarayyar kasar, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Sanata Adamu ya fallasa waɗanda su ke ɗaukar nauyin zanga zanga

Yanzu yanzu: Farfesa Yakubu ya sauka daga kujerar shugaban INEC, yana jiran tsammani
Yanzu yanzu: Farfesa Yakubu ya sauka daga kujerar shugaban INEC, yana jiran tsammani Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Ahmed zai yi aiki a matsayin Shugaban rikon kwarya har zuwa lokacin da Majalisar dattawa za ta tabbatar da sake nada Farfesa Yakubu a matsayin shugaban INEC.

KU KARANTA KUMA: Neman mafita: An bankaɗo wani gwamnan PDP yana shirin komawa APC a wannan makon

A baya mun kawo cewa Shugaban INEC mai sauka, Farfesa Mahmood Yakubu zai mika ragamar ma'aikatar ga wani baturen zabe da zai yi rikon kwarya, har sai majalisar tarayya ta tabbatar da kara nadinsa a matsayin shugaban INEC din ko kuma akasin hakan.

Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya kara zabar Yakubu, ya mika sunansa ga majalisar tarayya don tabbatar dashi, dama wa'adin mulkinsa na farko zai kare ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba.

Ana sa ran zai mika ragamar mulkin hukumar ga kwamishinonin da nasu wa'adin bai kare ba.

Akwai wasu kwamishinoni 5 da suka yi wa'adi biyu don haka basu da damar kara wani wa'adin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel