Da duminsa: Buhari ya sabunta nadin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
- Bayan ganin wa'adin mulkin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na neman karewa, Buhari ya sabunta nadinsa
- Kwatsam sai ga sanarwar sabunta nadin Farfesa Mahmood Yakubu a karo na biyu, inda zai kara yin wasu shekaru 5 a kan kujerar
- Duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ba-zata, hakan bai hana kowa tofa albarkacin bakinsa ba
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, don sake yin shekaru 5 a kan kujerar.
Bayan wa'adin mulkinsa na haramar karewa, shugaban kasar ya sake nada shi. Wasu suna kawo sunayen mutane da dama da suke tunanin shugaban kasa zai nada, ashe ba ta nan gizo ke saka ba.
Idan ba'a manta ba, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya hau kujerar bayan saukar Farfesa Attahiru Jega.
Farfesa Mahmood, kamar yadda aka ga ya tafiyar da zabukan 2017, ya tafiyar da mulkinsa cikin adalci da natsuwa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shayar da kowa mamaki bayan kara nada shi a wannan kujera,matsayin, duk da kowa yasan kujera ce mai hatsari da kuma bukatar nutsuwa kwarai.
KU KARANTA: Kotu ta umarci tsohuwar matar Atiku Abubakar da ta karba rikon 'ya'yansu 3
KU KARANTA: Lamarin Kogi ya kazanta, an cigaba da sace-sace a Abuja da Calabar
A wani labari na daban, Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Buratai, ya yi wani taro da manyan shugabannin rundunar soji, duk wasu GOC da kwamandojin filin daga.
Kamar yadda The Nation suka tattaro bayanai akan taron da akayi a hedkwatar tsaro a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba.
Kamar yadda jaridar ta ruwaito, Buratai ya ce wa manyan jami'an soji su tabbatar sun zama masu juriya, don hargitsa Najeriya ba nasu bane.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng