DSS su ka dauke takardun da CCB ta ke nema inji Lauyan Ibrahim Magu
- Ana bukatar Ibrahim Magu ya gabatar da bayanai game da kadarorinsa
- Tsohon Shugaban na EFCC ya ce DSS sun tattara takardun da ake nema
- A dalilin hakan, Lauyan Magu ya ce babu abin da zai kai shi gaban CCB
Tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya yi karin haske game da abin da zai hana shi bayyana gaban CCB domin ya kare kansa.
Ibrahim Magu ta bakin Lauyansa, Wahab Shittu, ya bayyana cewa ‘bata lokaci’ ne ya hallara gaban CCB.
Wahab Shittu ya ce a lokacin da aka kama Ibrahim Magu, wasu daga cikin takardun da su ka shafi bayanan kadarorin da ya mallaka, su na ofishinsa.
KU KARANTA: Laifin sata: Kotu ta aika Fasto zuwa gidan kurkuku
Barista Wahab Shittu ya ke cewa jami'an DSS sun yi gaba da wadannan takardu bisa umarnin kwamitin shugaban kasa a lokacin da Magu ya ke tsare.
Magu ya ke cewa ba zai yiwu ya iya tsaya wa gaban CCB dauke da takardun da ake bukata bayan suna hannun jami’an DSS da kwamitin shugaban kasa ba.
Tsohon shugaban na EFCC ya bukaci CCB ta tsawaita gayyatar da ta yi masa har zuwa lokacin da takardun na sa za su bar ofishin DSS, su shigo hannunsa.
Ana bukatar Magu ya fito da takardun bayanai game da kadarorin da ya mallaka tun daga lokacin da ya fara aikin gwamnati zuwa yanzu da ya bar EFCC.
KU KARANTA: N500, 000 sun raba ‘Daliban ABU Zaria da ‘Yan bindiga
Sauran takardun da ake bukata daga hannun Magu wanda ya rike EFCC a matsayin shugaban rikon kwarya sun hada da takardun samun aiki da na albashi
CCB ta na zargin Magu da saba dokar kasa da kin bin kundin tsarin mulki wajen bayyana kadarorin da ya mallaka, don haka ake shirin a bincikesa.
A ranar Juma'a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi cikakken sakamakon binciken da aka dade ana gudanarwa kan aikin tsohon shugaban na EFCC.
Tsohon Alkalin babban kotun daukaka kara, Ayo Salami da kwamitinsa sun binciki zargin da ke kan Ibrahim Magu kamar yadda shugaban kasa ya bada umarni.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng