Yadda Miyagu su ka zo Masallaci da ‘takarda’ da rana tsaka suka sace Masallata
- Ta’adin Miyagu a Zamfara ya kai inda ya kai, ana kashe na kashewa rana-tsaka
- ‘Yan bindiga sun sace Liman da wasu Mamunsa yayin da suke sallah a Zamfara
- Wadannan ‘Yan bindiga su na yawo ne dauke da sunayen wadanda za su hallaka
A ranar Juma’ar da ta wuce ne wasu miyagun ‘yan bindiga su ka shiga jihar Zamfara, inda suka yi awon-gaba da Bayin Allah da ke tsakiyar ibada.
Rahotannin da mu ka samu dazu sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun zo wurin ibadan ne dauke da jeringiyar sunayen wadanda za su kashe.
Bayan sun dauke mutane fiye da 100 daga masallacin, da aka shiga daji, ‘yan bindigan sun zabi wasu tsirarrun mutane da su ka harbe nan-take.
KU KARANTA: An gao gawar Shugaban APC da aka kashe
Audu Bulama Bukarti, masanin shari’a kuma kwararre a harkar tsaro, ya bayyana yadda wadannan miyagu su ka yi barnar da su ka yi a Zamfara.
Bulama Bukarti ya rubuta: “A ranar Juma’a da ta wuce, ‘yan bindiga sun kutsa wani masallacin Juma’a a Dutsen-Gari, jihar Zamfara, su ka yi awon gaba da mutane sama da 100 da ke sallah.”
“Da aka isa daji, sai su ka kira sunayen mutane 20 daga cikin wata takarda da su ka tafi da ita, su ka kashe mutane biyar, sannan su ka saki ragowar.”
Barista Bulama Bukarti ya ke cewa ko ‘yan ta’addan Boko Haram ba su yi irin wannan ta’adin ba.
KU KARANTA: N500, 000 sun raba ‘Daliban ABU Zaria da ‘Yan bindiga
Bukarti ya bayyana wannan ne a shafinsa na shafinsa na sada zumuntar zamani na Facebook. An samu wadanda su ka gaskata wannan magana.
Bayan haka, Bukarti wanda yanzu haka ya ke ketare, ya tabbatar da cewa daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da aka sace sun dawo gidajensu.
A makon da ya gabata kun ji yadda ‘Yan bindiga su ka kashe wani Mai Unguwa a yankin Zangon Kataf da ke kudancin jihar Kaduna inda ake ciki.
Bayan haka, Miyagun sun harbe ‘dansa har lahira, sannan sun bindige matarsa da 'yarsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng