Iyakarmu da Jami’an tsaro sai dai ‘Allah ya bada sa’a’ inji Iyayen ‘Yan Makaranta

Iyakarmu da Jami’an tsaro sai dai ‘Allah ya bada sa’a’ inji Iyayen ‘Yan Makaranta

- Wadanda aka sace masu yara a hanyar Abuja sun biya kudin fansa, sun fito

- Iyalan wadannan mutane sun ce babu abin da jami’an tsaro su ka iya yi masu

- Kusan duka ‘yanuwan wadannan daliban jami’a su ka biya akalla N500, 000

Bayan kwana shida a tsare, masu garkuwa da mutane sun fito da wasu dalibai tara na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da su ka shiga hannunsu.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa sai da iyayen ‘yan makarantar su ka biya N500, 000 zuwa N800, 000 kafin a fito masu da ‘ya ‘yansu a ranar Asabar.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, miyagun sun saki ‘yan makarantar ne a wani daji da ke kusa da kauyen Maru, a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Christian John, wanda ‘yaruwarsa Elizabeth John ta na cikin wadanda aka yi garkuwa da su, ya shaida wa jaridar cewa sun biya kudi kafin a fito da ita.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe wani Mai Unguwa a Kaduna

Da jaridar Punch ta yi yunkurin tuntubar jami’ar ABU Zaria, darektan hulda da jama’a na makarantar, Auwalu Umar bai bada wasu karin bayanai ba.

Malam Auwalu Umar ya nuna bai da masaniya ko an biya kudin fansa, amma ya tabbatar da cewa duka wadannan dalibai tara da aka sace, sun samu ‘yanci.

Iyalan da wannan musiba ta hau sun ce sun dauki wadannan kudi ne a jaka, daga nan sai aka yi masu bayanin inda za su kai kudin kafin su iske ‘ya ‘yansu.

Da ake bayanin inda aka samu daliban, wani ya ce an boye su ne a wani daji a hanyar kauyen Moro da ke kusa da garin Gwagwada, daf da sansanin NYSC.

KU KARANTA: Katsina: ‘Yan bindiga suna neman N100m a kan Jami’an ‘Yan Sanda 6

Iyakarmu da Jami’an tsaro sai dai ‘Allah ya bada sa’a’ inji Iyayen ‘Yan Makaranta
An yi garkuwa da ‘Yan Makaranta a Kaduna Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“Mun yi tafiyar mintuna 30 a daji, daga nan mu ka samu wasu a kan babur, mu ka hau, aka cigaba da wata tafiyar kusan mituna 30 a cikin kungurmin daji.”

Ya ce bayan an duba jikinsu, sai aka tafi aka kirga kudinsu, daga nan kowa ya rika fadan sunan wanda ya zo ceto bayan an tabbatar da kudinsa sun cika.

Bayan kudi, miyagun sun karbi lemu da madara, sannan akwai wanda masu garkuwan su ka ba kyautar N30, 000 domin ta saye sabulu, ganin ta yi butu-butu.

Idan za ku tuna, an tare wadannan ‘yan makaranta ne tsakanin hanyar Akilubu da Gidan Busa a kan titin Abuja a lokacin da su ke hanyar zuwa wata gasa.

Da farko an bukaci Naira miliyan 270 daga hannun ‘daliban, a karshe da-dama su ka biya N500, 000, yayin da wasu su ka ce sun bada abin da ya kai N800, 000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel