Gwamnoni, tsaffin ministoci da jiga-jigai 'yan siyasa sun ziyarci Jonathan yayinda ya cika shekara 63
- Bikin taya murnar ranar zagayowar haihuwar tsohon shugaba Jonathan ya samu halartar manyan jami'an gwamnatinsa da gwamnati mai ci
- Daga cikin mahalarta taron akwai gwamnonin Jigawa, Yobe, da Ebonyi, Badaru, Mala Buni da kuma Dave Umahi da kuma tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo
- Jonathan ya godewa mahalarta taron da matarsa ta shirye tare da yabawa matar tasa da sauran mutane da ya ce sun yi sammako don taya shi murna
'Yan Najeriya da daga bangarori daban daban sun kaiwa tsohon shugaba Jonathan ziyara a gidansa da ke Abuja don taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Bakin sun hada da tsofaffin masu taimaka masa da gwamnoni masu ci da tsofaffi daga jam'iyyan PDP da APC, sun kuma gode masa kan abubuwan alherin da ya ci gaba da aiwatarwa don wanzar da zaman lafiya da martabar Najeriya tun bayan barin mulki.
Da ya ke jawabi tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya bayyana Jonathan a matsayin gogaggen jagoran siyasa kuma jigo ga Najeriya.
DUBA WANNAN: Gwamna Bala Muhammad ya ƙaryata rade-radin ficewarsa daga PDP
Da yake martani kan sakonnin fatan alherin, Jonathan ya godewa wanda suka halarci taron tare da yabawa matarsa da sauran iyalai da suka hada masa shagali da kuma addu'o'i a bikin zagayowar haihuwarsa.
Ya ce: "Wannan safiyar (Juma'a), na sauko da misalin 6:00 na safe kuma na tarar da mutane a zaune suna jira na suyi min addu'a don tayani murna.
"Wannan na nufin cewa wadannan mutane sun baro gidajen su tun kafin 5:30 na safe don su zo gidana da wuri.
"Kuma tun daga wannan lokacin har karwa wannan yammaci (Juma'a), muna ta ci gaba da karbar baki.
"Ina mika sakon godiya ga mata ta data shirya wannan shagali sannan ina godewa duk wanda ya zo ba tare da sanarwa a gidajen jarida ko tura sakonni don gayyatar baki," a cewar shugaba Jonathan.
KU KARANTA: Har kyautan N1m na taba bawa matata amma hakan bai hana ta bin maza ba, Miji ya fada wa kotu
Daga cikin dubban mutanen da suka ziyarci Jonathan don taya shi murnar akwai gwamnan Bauchi Bala Mohammed, da gwamnan Yobe, Mala Buni, Atiku Bagudu na Kebbi, gwamna Badaru Abubakar na Jigawa, gwamna Dave Umahi na Ebonyi da tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo.
Taron ya kuma samu halartar tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamami da tsofaffin ministoci da dama da suka hada da tsohon ministan lafiya da ya yaki Ebola a Najeriya, Onyebuchi Chukwu da wasu da dama.
Sauran sun hada da tsohon shugaban ma'aikata, Mike Ogiadhome, John Opara, tsohon shugaban hukumar Kula da Harkokin Hajjin Kiristoci, da mai bashi shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak.
A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng