An tono wasikar da Marigayi Jafar Adam ya rubutowa Diyarsa shekaru 20 da suka wuce

An tono wasikar da Marigayi Jafar Adam ya rubutowa Diyarsa shekaru 20 da suka wuce

  • Zainab Jafar Mahmud Adam ta bankado wata wasika da Mahaifinta ya aiko mata
  • Wannan Baiwar Allah ta ce ta ga wasikar da aka rubuto a 2002 ne cikin littatafanta
  • ‘Diyar Shehin ta bayyana rashin Mahaifi a matsayin babbar gibi a rayuwar Duniya

Kano - ‘Diyar Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam, Zainab, ta lalubo wata wasika da mahaifinta ya taba rubuto mata a ranar 3 ga watan Fubrairun 2020.

Legit.ng Hausa ta samu labari Zainab Jafar Mahmud Adam ta daura hoton wannan wasika ne a shafin Facebook a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta, 2021.

Malama Zainab Jafar Mahmud Adam ta ce mahaifin na su ya aiko mata wannan takarda ne lokacin da yake karatun digirgir a birnin Khartoum, Sudan.

Wasika ta tuna mata da mahaifinta

“Shekaru 19 kenan da watanni mahaifina ya rubuto min wasikar nan daga qasar Sudan, lokacin yana karatun shi na Masters degree a can.”

Kara karanta wannan

Dadiyata: Iyaye da Iyali sun koka game da halin tashin hankalin da suka shiga a shekaru 2

“Yau babu zato babu tsammani na ci karo da ita cikin wasu tsofaffin littafaina, ina karanta wa sai na ke jin ina ma ina da damar da zan sake samun irin wannan wasika daga gareshi yanzu amma inaa!!”
“Sai nake jin kamar yanzu ne ya rubuto mani ita saboda gamammun sakonnin da ke cikinta da zansu amfane ni tsawon rayuwata.”

An tono wasikar da Marigayi Jafar Adam
Wasikar Malam Jafar Hoto: Engr Basheer Adamu Aliyu
Asali: Facebook

“Ina karantawa cike da tunanin irin yadda rayuwata ta kasance da shi a wancan lokutan, na yi rayuwa mai cike da kulawa, gata, tarbiyyantarwa, bada kariya, ilimantarwa, uwa uba kuma kauna ta musamman daga gareshi wadda ba zan taba mantawa da ita ba har na koma ga Allah.”

Bayan kewa da yabon da ta yi wa mahaifinta, Zainab Jafar Adam ta ce rashin mahaifi babban gibi ne, sannan ta yi addu’a Allah ya yi masa rahama, ya ba shi aljanna.

Wasikar da Marigayi Jafar Adam ya rubuto
Wasikar Malam Jafar Hoto: Engr Basheer Adamu Aliyu
Asali: Facebook

Menene wasikar Marigayin ta kunsa

Shehin malamin ya ba ‘diyarsa shawara ta dage da tsoron Allah (SWT) a kowane hali, ta tsaida sallah a kan lokaci, kuma ta maida hankali wajen haddar Qur’ani.

Kara karanta wannan

Likitoci a Najeriya zasu tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Har ila yau, wannan wasika a cikin harshen larabci ta yi kira ga Zainab Jaafar ta zama mai biyayya ga mahaifiyarta, tare da yin hakuri da sauran ‘yanuwanta.

Injiniya Basheer Adamu Aliyu ya fassara abin da takardar ta kunsa, sannan ya wanke hoton wasikar.

Bayan shekaru biyar aka kashe Sheikh Jafar Adam

A watan Afrilun shekarar 2007 wasu miyagun mutane suka harbe Sheikh Ja'afar Mahmud Adam a lokacin da ya ke limancin sallar asuba ranar Juma'a a Kano.

Babban ‘dan Marigayi Sheikh Ja'afar Adam, Saleem Ja'afar Mahmud Adam ya ce shi ne wanda ya yi magana da Malam a cikin iyalinsa a asubar da aka kashe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel