Mutane 18 sun rasu a hadarin kwale-kwale a Bauchi

Mutane 18 sun rasu a hadarin kwale-kwale a Bauchi

- Kwale-kwale ya kife da mutane 23 inda 18 suka rasa rayukansu a Bauchi

- Daga cikin wanda hadarin ya afkawa akwai yara yan shekara 16 zuwa 18

- An ceto matukin da wasu mutane 4 cikin mawuyacin hali inda aka garzaya dasu asibiti

Bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Mutane 18 sun rasu a hadarin kwale-kwale
Mutane 18 sun rasu a hadarin kwale-kwale
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari ta waya sun tattauna

Daga cikin wanda suka rasu akwai yara tsakanin shekara 18 da 16.

Wanda hadarin ya rutsa da su an dauko su ne daga kauyen Zango Majiya a karamar hukumar Itas Gadau zuwa gonakinsu lokacin da kwale-kwalen ya kife kuma suka nutse a tsakiyar Kogin Buji.

KU KARANTA: Wasu mazauna Kaduna sun soki harajin cigaba na N1,000 da gwamnati ta sakawa duk baligai

Kakakin yan sandan ya ce an ceto mutane biyar cikin su harda matukin cikin mawuyacin hali sannan an garzaya da gawawakin zuwa babban asibitin Itas don gudanar da bincike.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wasu magidanta a karamar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi sun koka kan karancin kororon roba a yankin wadda ke taimaka musu wurin bada tazarar haihuwa.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Cibiyar Lafiya ta mazabar Kafin Madaki, Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da ya yi wa manema labarai jawabi.

"Mu a matsayinmu na kwamiti, mun dukufa wurin wayar da kan al'umma kuma da dama cikinsu sun rungumi wannan tsarin sosai.

"Maza a yanzu suna fitowa fili su nemi a kawo musu kororon roba don su taimakawa matansu, sai dai a halin yanzu wadanda muke da su nan sun kare," a cewarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164