Har kyautan N1m na taba bawa matata amma hakan bai hana ta bin maza ba, Miji ya fada wa kotu

Har kyautan N1m na taba bawa matata amma hakan bai hana ta bin maza ba, Miji ya fada wa kotu

- Kotu ta raba auren da ya shekara 8 tare da mika alhakin kula da yara biyu da ke tsakanin ma'auratan a hannun mahaifiyarsu

- Mijin ya bayyana cewa wata rana, nayi mata fada akan ta bar gida da yara ta fice tsawon kwanaki uku amma sai ta fasa kwalba a kansa

- A nata bangaren matar wadda ke zaune a Total garden da ke Ibadan, ta ce mijn nata ɗan giya ne kuma mai neman mata

Wata kotun gargajiya da ke zaman ta a Mapo dake Ibadan, ta raba auren shekara takwas tsakanin Julius Akintola da tsohuwar matar sa bisa zargin zina da kuma rashin soyayya.

Da yanke hukunci, alkalin kotun, Chief Ademola Odunade, ya ce kotun ta raba auren saboda kawo karshen rikici tsakanin Julius da Ejide sakamakon rashin imanin wanda ake karar.

"Auren tsakanin Julius da Ejide an raba shi saboda samar da zaman lafiya kuma an mika kula da yayan su biyu a hannun wanda ake ƙarar.

"Mai ƙara zai dinga biyan kuɗin ciyarwa duk wata Naira 8,000 tare da ɗaukar nauyin karatun su da sauran bukatu da suka zama dole," a cewar Odunade.

Na bawa matata kyautar N1m daya a kudin cacar dana ci, yanzu ta ha'inceni
Na bawa matata kyautar N1m daya a kudin cacar dana ci, yanzu ta ha'inceni. Hoto @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Alkalin ya kuma shawarci masu shirin yin aure da su lura kada su fada hannun na banza.

Tun da farko, Akintola, mazaunin yankin Oke-Labo a Ibadan ya shaidawa kotu cewa ya gaji da auren su da Ejide saboda tana bin maza a waje.

"Ban taba sanin mazinaciya na ɗauko a matsayin mata ba, lokacin da nake cikin daula ina bawa Ejide fiye da abin da ta bukata.

"Kai har Naira miliyan guda na bata lokacin da na ci kuɗin caca.

"Sai dai, Ejide ta zama dadiro bayan da kusawanci ya durkushe, ta na kwana da wasu mazan," a cewar sa.

Ya bayyana cewa wani dadiron ta yana zuwa ya dauke ta su fita tsakar dare kuma a gaban sa ake waya.

"Ya taɓa cemin wai ni ce sanadiyar faɗuwa da yake yi a caca saboda haka sai na bar masa gidansa," a cewar ta

KU KARANTA: A dena kira na 'Special One', Mourinho ya bayyana sabon sunan da ya ke so

"Abin takaici, Ejide tana nuna sha'awar ta lokacin da take tattaunawa ta waya, kuma tana shan magani da zai kara mata karfin sha'awa.

"Wata rana, nayi mata fada akan ta bar gida da yara ta fice tsawon kwanaki uku; sai Ejide ta ɗauki kwalba ta fasa min a kai.

Ejide, wadda ke zaune a Total garden da ke Ibadan, ta ce mijn nata dan giya ne kuma mai neman mata.

"Tunda Julius ba ya ɗaukar nauyi na kuma akwai nisa daga gida zuwa inda nake aiki, sai, na yanke shawarar zan dinga bin mutumin.

"Julius yakan saka min 'magun' yadda duk wanda ya kusanceni zai mutu."

Magun wani maganin gargajiya ne da ke cutar da duk wanda ya kusanci mace.

A wani labarin, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164