Gwamnan Kwara ya gabatar da kudirin haramta wa tsofaffin Gwamnoni fansho

Gwamnan Kwara ya gabatar da kudirin haramta wa tsofaffin Gwamnoni fansho

- Gwamnan jihar Kwara ya gabatar da kudirin hana tsofaffin Gwamnoni fansho

- AbdulRahman AbdulRasaq ya kawo wannan kudiri ne domin rage kashe kudi

- Idan har Majalisar jihar ta amince, su Bukola Saraki za su daina karbar fansho

A ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, gwamna AbdulRahman AbdulRasaq na jihar Kwara ya gabatar da kudirin da zai haramta wa tsofaffin gwamnoni fansho.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta ce Mai girma gwamna AbdulRahman AbdulRasaq ya gabatar da wannan kudiri ne a gaban majalisar dokoki.

Kudirin da gwamna mai-ci ya kawo, ya na neman a dakatar da biyan duka tsofaffin gwamnoni da mataimakansa makudan kudi duk wata da sunan fansho a jihar.

KU KARANTA: Sanwo-Olu zai daina biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu fansho

Shugaban majalisar dokokin, Yakubu Danladi ya bada sanarwar abin da ya kai gwamnan gabansu.

NAN ta ce Rt. Hon. Yakubu Danladi ya bayyana wannan ne yayin da ya ke karanta jawabin da gwamna AbdulRahman AbdulRasaq ya yi wa ‘yan majalisar jihar.

Gwamnan ya ke cewa ya shigo da wannan kudiri ne a dalilin kukan da jama’an jihar su ke yi.

Rt. Hon. Yakubu Danladi ya ce wannan kudiri zai taimaka wa gwamnatin Kwara wajen cinma burinta na tsantseni da rage facaka wajen batar da dukiyar al’umma.

KU KARANTA: Tinubu ba ya adawa da daina biyansa fansho a Legas

Gwamnan Kwara ya gabatar da kudirin haramtawa tsofaffin Gwamnoni fansho
Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: von.gov.ng
Asali: Twitter

Daukacin ‘yan majalisar dokokin sun yi na’am da wannan kudiri, kuma ya samu zarce matakin farko. Yanzu za a aika kudirin zuwa ga kwamitin sha’ani da dokoki.

A zama na gaba da za ayi, ‘yan majalisa za su sake sauraron kudirin, inda daga nan za a san ko za a fitar da shi daga majalisa, ko zai samu shiga zuwa mataki na gaba.

Tun a baya aka ji cewa Gwamnan Jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya sanar ta shafinsa na Twitter, gwamnati za ta kawo karshen biyan tsofaffin gwamnoni fansho.

Gwamna Abdulrazak yace gwamnatinsa na bukatar kudi domin inganta rayuwar al'ummar jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel