A karon farko, Tinubu ya magantu a kan daina biyan tsoffin gwamnonin Legas fansho
- Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya yaba wa gwamnan jihar legas, Sanwo-Olu a kan kasafinsa na 2021
- Dama gwamna Sanwo-Olu ya bukaci a dakile biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu fansho
- A cewar Tinubu, yin hakan almubazzaranci ne, yana tare da Sanwo-Olu dari bisa dari a kan wannan matakin
Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya taya gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, murna a kan shirinsa na dakatar da ba wa gwamnoni da mataimakansu fansho, a matsayin matakan dakile almubazzaranci.
A wata wallafa da Tinubu yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Laraba, ya ce: "Ina taya Gwamna Sanwo-Olu murna a kan kasafin da ya tsara, wanda dama hakan yayi daidai. Wannan kasafin zai taimaki mutanen jihar Legas, sannan zai taimaka wurin bunkasa jihar."
"Ina so in shawarci gwamnan da yayi gaggawar dakile fanshon gwamnoni da mataimakansu," cewar Tinubu.
Ya kara da cewa, "Ina matukar farin ciki da wannan matakin da gwamnan ya dauka, ina tare da shi dari bisa dari. Ina shawartar duk wasu 'yan jam'iyyar APC da suyi koyi dashi."
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gwamna Sanwo-Olu ya nemi a rushe biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu fansho a cikin kasafin 2021, don yin hakan almubazzaranci ne.
KU KARANTA: Ba za a samu rashin abinci a karkashin mulkina ba, Buhari
KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yar kunan bakin wake tare da wasu mayakan ta'addanci
A wani labari na daban, an damki wanda ya hada bidiyon bogi na auren minista Sadiya Umar Faruk da shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Janairu. An gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin hada bidiyon bogi.
Bayan zurfafa bincike, Hukumar DSS ta samu nasarar damko Kabiru Mohammed tun watan Janairu, amma bata gurfanar dashi gaban kotu ba sai ranar Talata.
Ta ce tana zarginsa da hada bidiyon na bogi, wanda hakan ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng