Sanwo-Olu zai soke biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kuɗin fansho
- Gwamna Babaajide Sanwo-Olu na jihar Legas yana son a dena biyan tsaffin gwanoni da mataimakansu kudin fansho
- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin gababatarwa Majalisar Jihar kasafin kudin shekarar 2021
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a ranar Talata ya sanar da niyyansa na soke dokar biyan fansho na 2007 da ke bada damar biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho.
Ya sanar da hakan ne yayin da ya ke gabatar da kasafin kudi na shekarar 2021 ga Majalisar Jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.
KU KARANTA: Harin Musulmin Ƙabilar Igbo: MURIC ta buƙaci a gurfanar da Rev Fr. Onah
DUBA WANNAN: Wani dan shekara 69 ya yi ikirarin ya saki matarsa don ta zabi Joe Biden a zaben Amurka
Sanwo Olu ya ce zai aike wa majalisar jihar Legas kudirin doka na neman amincewarsu game da batun.
A cewar Sanwo Olu, soke biyan tsaffin gwamnoni da mataimakan gwamnoni kudin fansho din zai rage kudaden da gwamnati ke kashewa.
Ya ce, "Mai girma Kakakin Majalisa da mambobin majalisa, bisa tsarin rage kudaden da gwamnati ke kashewa da yi wa talakawa aiki, za mu aiko da kudin dokar ga majalisa na neman soke dokar (Payment of Pension Law 2007) da ta bada daman biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho."
A wani labarin, barayi sun sace kaya masu tsada da kudinsu ya kai Euro 600,000 daga gidan 'yar gidan sarautar Saudiyya da ke kasar Faransa kamar yadda wani na kusa da masu bincike ya sanar a ranar Juma'a.
'Yar gidan sarautar mai shekaru 47 ba ta shiga gidan ba tun watan Agusta amma da shigar ta sai ta gano an ce mata jakkuna, agoguna, kayan ado na zinari da wasu tufafin da kudinsu ya kai Dallar Amurka 720,000.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng