Soyayya ruwan zuma: Labarin yadda wani mutum da aka haifa da tawaya ya hadu da kyakyawar matarsa

Soyayya ruwan zuma: Labarin yadda wani mutum da aka haifa da tawaya ya hadu da kyakyawar matarsa

- Wata mata mai suna Mayfair Clements ta tuna yadda ta fada tarkon son mijinta, Winston Ben

- Bayan haduwarsu a wani taro, Mayfair ta bayyana cewa su duka biyun sun san cewa sun fada wani tarko mai ban al’ajabi

- An haifi angonta, Ben da tawaya amma hakan bai hana Mayfair kulla alaka da shi ba, lamarin da har ya kai su ga aure

- Ta wallafa wasu hotunansu a tare sannan ta raka hotunan da sako mai sace zuciya

Soyayya abune mai dadi da ya cancanci a ci moriyarsa tare da mutumin da ya dace a cikin kowani irin yanayi kuma hakan ne ya kasance a labarin wata matashiya mai suna Mayfair Clement.

A wani wallafa da ta yi a shafin Instagram, ta jinjinawa mijinta mai suna Winston Ben sannan ta tuna yadda suka hadu har ya kai su da zama masoya.

Winston Ben Clements wanda aka haifa da tawaya kuma yake zaune a kan keken guragu ya hadu da Mayfair a wajen wani taro kuma bai wani jima ba ya sace zuciyarta.

Soyayya ruwan zuma: Labarin yadda wani mutum da aka haifa da tawaya ya hadu da kyakyawar matarsa
Soyayya ruwan zuma: Labarin yadda wani mutum da aka haifa da tawaya ya hadu da kyakyawar matarsa Hoto: mayfairclements
Asali: Instagram

A wallafar da ta yi a Instagram, Mayfair ta bayyana cewa sun fada wani tarko mai wuyar sha’ani kuma dukkaninsu sun ji hakan a cikin bargon kashinsu.

KU KARANTA KUMA: Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera

Ta wallafa:

“Auri wanda zai zamo duk wani sassa na jikinka. Na tuna ainahin lokacin da na fada tarkon sonka. Mun fara hadewa ne a taron @tldmmastermind amma duk mun ji wani yanayi a cikin bargon kasusuwanmu – mun fada cikin wani yanayi mai ban al’ajabi. Bayan nan mun yi hira tsawon daren, duk mun gaji sannan muka ji ruhinmu sun hade kuma farkon ganin da nayi maka kenan. Bi ma’ana na ganka. Ba wai a matsayin mai maganar ba."

KU KARANTA KUMA: Wike da wasu gwamnonin PDP suna shirin dawowa APC, In ji Gwamna Yahaya Bello

Ta ci gaba da cewa:

“Ba wai a matsayin mai karfafa gwiwa ba. Ba wai a matsayin mutumin da ke zaune a keken guragu ba. Ba ma a matsayin abokina ba. Na ganka. Har na yi ta al’ajabin yadda Ubangiji ya tsara ruhinka da kyawu. Mun kasance abokai a wannan lokaci. Amma ba zan yi karya ba, tunanin da nake ta yi shine – “kai jama’a wannan mutumin zai zamo uba kuma miji daya tamkar da dubu. Jim kadan bayan nan Winston ya fada mani abunda yake ji game da ni “ina so ki zama cikin tawagata har abada” bayan watanni tara, ya aiwatar da hakan.”

A gefe guda, bidiyon wata kyakyawar amarya ya sanya yan Najeriya da dama dariya a shafin soshiyal midiya.

A bidiyon wanda Legit.ng ta samo a shafin Instagram, an gano amaryar da angonta suna ta dauke dauken hotunan auransu.

Mai daukarsu hoton ya bukaci angon ya mannawa amaryarsa sumba a kumatu amma sai ta yi gaggawan janyewa, inda ta fada wa mijin cewa kada ya taba mata kwalliyarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel