Wike da wasu gwamnonin PDP suna shirin dawowa APC, In ji Gwamna Yahaya Bello
- Gwamna Yahaya Bello ya kaddamar da cewar wasu gwamnonin PDP za su koma jam’iyyarsu ta APC kwanan nan
- A ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba ne, David Umahi na Ebonyi ya yi bankwana da PDP gaba daya sannan ya rungumi APC
- Bello ya bayyana cewa Gwamna Wike ne gwamnan PDP na karshe da zai sauya sheka zuwa APC
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa akwai Karin gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke shirin dawowa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Yahaya Bello ya bayyana hakan ne yayinda yake martani ga sauya shekar Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi daga PDP zuwa APC.
Gwamnan na Kogi ya kara da cewa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, shine zai zamo karshen komawa jam’iyyar mai mulki.
KU KARANTA KUMA: Yadda Buhari ya sanya ni barin PDP zuwa APC, Gwamna Dave Umahi ya magantu (Bidiyo)
Ya bayyana Umahi a matsayin wanda ya aminta da APC tun lokacin da yake a matsayin dan babbar jam’iyyar adawa ta kasar, PM News ta ruwaito.
“Na fadi da dadewa, ba a yau da jam’iyyar PDP ke fuskantar wasu matsaloli ba; na bayyana cewa akwai gwamnoni 10 daga jam’iyyar adawa da za su dawo APC.
“Mun ga daya; dayan da yake tamkar 10, ya dawo cikinmu, saura tara. Ku ce na fada; bana karya, ba zan taba karya ba, kuma bazan taba yaudarar kowa ba,” cewar gwamnan na Kogi kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Dan baiwa: Kamfanin motoci na sake kera motar da wani matashin yaro dan shekara 18 ya kera
Bello ya ci gaba da cewa"Umahi na tare da mu, saura na nan zuwa.
“Tuni sauran gwamnoni suka fara kwankwasa kofa. Suna akan hanyarsu. Za mu bayyana su daya bayan daya.
“Wike na iya zama mutum na karshe da zai dawo tafiyar APC. Saura na nan sun yi layi.”
A gefe guda, Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, ya ce ya zama abun zargi a jam’iyyar PDP saboda kawai ya ki caccakar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng