Umar Dagona ya yi zarra a babbar gasar kimiyya da aka shirya a Abuja

Umar Dagona ya yi zarra a babbar gasar kimiyya da aka shirya a Abuja

- Umar Usman Dagona ne ya zo gwarzon gasar Imaginechemistry na 2020

- Kafin yanzu ba a san mutanen Arewacin Najeriya da wannan kokarin ba

- Matashin ya na da shaidar NCE, amma bai samun wani aiki mai tsoka ba

Wani Bawan Allah daga jihar Yobe da ya wakilci mutanen Najeriya a gasar ilmin sinadarai da aka gudanar a garin Abuja, ya samu nasara mai tarihi.

Rahotanni da-dama sun tabbatar da cewa Malam Umar Usman Dagona ya zo na daya a wannan katafaren gasa da aka shirya da kasashen Duniya.

Umar Usman Dagona ya na cikin wadanda su ka tsallaka zuwa matakin karshe na wannan gasa mai suna “Imaginechemistry" da aka yi kwanan nan.

KU KARRANTA: ASUU ta ce babu maganar komawa aiki a Najeriya

Mutumin da ya fito daga garin Gashua da ke arewacin jihar Yobe ya tashi da kyautar kudi na Dalar Amurka fam 400,000 (sama da Naira miliyan 150).

Umar Dagona ya yi karatun ilmin sinadarai ne a makarantar koyon aikin malanta na Umar Suleiman a Gashua, inda ya samu shaidar NCE a 2018.

Da wannan nasara, Umar Dagona ya nuna cewa mutanen arewacin Najeriya za su iya yin kafada-da-kafada da mutanen Kudu da su ka saba lashe gasar.

Dagona ya fada wa ‘yan jarida cewa: “Gasar ta na kunshe da mutane 1750 a zangon farko, amma mutane 255 ne kawai suka samu kai wa mataki na gaba.”

KU KARANTA: Muguwar cuta da ba ta jin magani ta kunno kai a Kogi

Umar Dagona ya yi zarra a babbar gasar kimiyya da aka shirya a Abuja
Umar Usman Dagona Hoto: /www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Da aka je matakin karshe kuwa, mutane 13 rak su ka rage, a haka ne Dagona ya zo na farko a gasar.

Duk da baiwar da Ubangiji ya yi wa Dagona, bai samu aikin yi a Yobe ba, hakan ta sa dole ya koma jihar Kano ya samu wata makaranta, ya na koyar wa.

A jiya kun ji yadda rashin imani ya sa wani Mai gida ya garkame matarsa tun 2016, a haka ta haifa masa yara uku yayin da ta ke tsare ba ta fita.

Wannan mutum ya daure matarsa tsawon shekarun nan ne saboda kawo masa karayar arziki

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng