Kiwon lafiya: Wata bakuwar cuta ta shiga Jihar Kogi, ta kashe Bayin Allah

Kiwon lafiya: Wata bakuwar cuta ta shiga Jihar Kogi, ta kashe Bayin Allah

- ‘Yan Majalisar Kogi sun ce an yi wata cuta da ke kashe Jama’a a Olamaboro

- Kawo yanzu ba a san daga ina cutar nan ta fito, ko a iya gano maganinta ba

- ‘Dan Majalisar Olamaboro ya bukaci gwamnati ta kawo karshen annobar nan

Majalisar dokokin jihar Kogi ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jiha su yi bincike game da sabuwar cutar da ta shigo gari a ‘yan kwanakin nan.

Bakuwar cutar da ba a kai ga gane lamarinta ba ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 50 a garin Olamaboro, Kogi.

Vanguard ta ce ‘yan majalisar jihar sun yi wannan kira ne yayin da su ka zauna a zaurensu da ke garin Lokoja a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba.

KU KARANATA: Masu garkuwa sun bar Kauye ana makoki, sun kashe Hakimi

Honarabul Anthony Ujah mai wakiltar mazabar Olamaboro a majalisar jihar ya fara kawo kukansa, ya ce cutar ta kai ga hallaka mutane har 50.

Anthony Ujah ya ce alamomin wannan muguwar cuta sun hada da ciwon kai, rikidewar idanu su yi ja-wur, gaza cin abinci da kuma wahalar yin bayan gida.

Wadanda su ka kamu da cutar nan su na fuskantar barazana wajen yin bawali da bayan gida.

Ujah ya ce mutanen kauyen Etteh da ke karkashin mazabarsa sun shiga cikin wani halin ban tausayi a sakamakon wannan cuta da ke hallaka matasa.

KU KARANTA: Abin da na yi da na ke jinyar COVID-19 - Gwamna Bello

Kiwon lafiya: Wata bakuwar cuta ta shiga Jihar Kogi, ta kashe Bayin Allah
Majalisar jihar Kogi Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

‘Dan majalisar ya ce har yanzu ba a san abin da ya ke jawo ciwon ba. Abin takaicin shi ne duk wasu magungunan gargajiya sun gagara aiki a kan cutar.

Likitoci su na aika wadanda su ka kamu da cutar zuwa dakunan shan magani da asibitoci da ke makwabta a yankunan Oguru da Okpo, amma duk a banza.

Kakakin majalisar, Prince Kolawole ya saurari batun, har ya sa aka yi tsit domin a tuna da wadanda cutar ta kashe daga watan Satumba zuwa yau.

Yau da safe kun ji cewa 'yan bindiga sun bukaci N270m kafin su saki daliban ABU Zaria da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa birnin tarayya Abuja daga Kaduna.

Wani daga cikin daliban na ABU Zaria da aka tare, ya samu ya tsere ya bayyana wannan jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel