‘Yan Sanda sun cafke wanda ake zargi ya tsare Matarsa har shekara 4 a daki

‘Yan Sanda sun cafke wanda ake zargi ya tsare Matarsa har shekara 4 a daki

- An damke wani Mutumi da ya rufe Mai dakinsa a gida har tsawon shekaru 4

- Wannan Magidanci ya na zargin Mai dakin tasa da jawo masa karayar arziki

- Sai da wannan mata ta yi shekaru hudu babu abin da ta ke ci sai burodi a gida

Jami’an ‘yan sandan jihar Delta, sun kama wani mutumi mai suna Ame Edjeket wanda ake zargi da laifin garkame matarsa ta aure na tsawon shekaru hudu.

Ame Edjeket mai shekara 41 ya tirke mai dakin ta sa ne inda ya rika galabaitar da ita a gidansu. Ma’auratan su na zaune ne a garin Orerokpe, a jihar Delta.

Jaridar Punch ta ce a lokacin da wannan Baiwar Allah da ta haifawa wannan mutumi ‘ya ‘ya takwas ta ke tsare, babu wani abincin da ake ba ta sai sunkin burodi.

KU KARANTA: Malamai sun nemi a rika hukunta masu batanci ga addini

Bayan haka mutumin ya hana uwar ‘ya ‘yan nasa amfani da bayan gida ko kuma yin wanka.

Ana haka ne sai labarin ta ya kai ga wata gidauniya da ake kira Behind Bars Defenders foundation, wanda su kuma su ka shiga binciken abin da ya ke faruwa.

Shugaban gidauniyar Behind Bars Defenders, Harrison Gwamnishu, ya bayyanawa ‘yan jarida cewa Ame Edjeket ya na zargin mai dakinsa da zama silar tsiyacewarsa.

Abin da ya ke da ban mamaki shi ne Mista Edjeket ya yi karatu har ya na da shaidar Difloma, kuma a irin wannan yanayi ne matarsa ta haifa masa yara har uku.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna ya yunkuro, ya na neman zuba jari a Arsenal

Gwamnishu ya ce: “Tayi shekaru hudu a daure. A cikin dakin da take bawali da bayan gida, a nan mijinta ya ke ba ta burodi, ba wai burodin kwalama ba, bugun-kato.”

Yanzu wannan mata ta na kwance a asibiti, yayin da shi mai gidan na ta ya ke hannun jami’an tsaro, inda ya yi ikirarin mai dakin ta sa da ta na da tabin hankali.

Kamar yadda ta ke faruwa a jihohi kamar Kano da Jigawa,

Hukumar Hisbah a Katsina ta kama giya fiye da 300 inda kuma ba ta yi wata-wata ba ta konasu.

A karkashin dokokin shari'ar addinin musulunci bai halatta a rika sha ko sayar da giya da sauran barasa ba. Ana amfani da wannan doka a wasu jihohin arewacin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel