Dan ƙwallon Najeriya ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a yayin buga wasa a Abeokuta

Dan ƙwallon Najeriya ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi a yayin buga wasa a Abeokuta

- Yusuf Usman Usein da ke buga wa Shooting Stars da Crown FC wasan ƙwallon ƙafa ya rasu

- Ɗan wasan da ke buga gaba ya tafi yana wasa da Gateway na Abeokuta ne sai ya yanke jiki ya faɗi

- A safiyar ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba ne Crown FC ta tabbatar da cewa Usein ya rasu

Ɗan ƙwallon Najeriya, Usman Yusuf, da ke buga wa ƙungiyar Crown Football da ke Ogbomoso, Oyo wasa ya rasu bayan ya yanke jiki ya faɗi yayin da suke buga wasa a Abeokuta a jihar Ogun.

Abin baƙin cikin ya faru ne a ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamban 2020 a filin wasa na Muda Lawal, Asero, Abeokuta.

Fitaccen dan kwallon Nigeria ya yanke jiki ya fadi yayin motsa jiki
Fitaccen dan kwallon Nigeria ya yanke jiki ya fadi yayin motsa jiki. Hoto: Tunji Alabi
Asali: Twitter

Yusuf wadda ke gwaji a Gateway United FC, ya buga kashi na farko na wasar da suke buga wa da Sliema Wandarers kafin afkuwar lamarin.

An ruwaito cewa likitocin da ke filin wasa sun farfaɗo da shi bayan ya yanke jiki ya faɗi. Daga nan aka garzaya da shi asibiti inda daga bisani ya rasu.

DUBA WANNAN: Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

Moses Ojewumi, jami'in watsa labarai na Gateway FC ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Litinin a Abeokuta.

Ya ce, "Usman Yusuf wanda ya zo gwaji ya buga kashi na farko na wasan da Gateway United FC ke bugawa da Sliema Wandarers a ranar Lahadi, a farko ya nuna alamu marasa kyau kuma likitan Gateway United ya duba shi.

"A daren ranar labari ya zo cewa rashin lafiyar ya sake dowowa, nan take aka kai shi asibitin Jihar inda ya rasu a can."

Ojewumi ya ƙara da cewa ɗan wasan bai nuna alamun bashi da lafiya ba lokacin da ya zo gwajin kuma bai mutu a sansanin bada horon wasa ba kamar yadda wasu suka yi kuskuren bada rahoto.

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel