Insight Dynamic Resources ya kalubalanci Amaechi da Ahmadu a Kotun Abuja

Insight Dynamic Resources ya kalubalanci Amaechi da Ahmadu a Kotun Abuja

- Wani kamfani, Insight Dynamic Resources Limited ya na karar gwamnatin Najeriya

- Kamfanin ya kai Ministan sufuri da shugaban BPP gaban wani babban kotun tarayya

- Ana zargin an saba doka wajen bada kwangilar titin jirgin kasan Maiduguri-Fatakwal

An shigar da Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi gaban babban kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin saba doka wajen bada kwangilar dogo.

Daily Trust ta ce ana zargin Ministan da saba wa dokar bada kwangila a aikin gyaran titin jirgin kasan Fatakwal zuwa Maiduguri da ake shirin yi.

Shugaban hukumar BPP na kasa, Mamman Ahmadu ya na cikin wanda wannan kamfani na Insight Dynamic Resources Limited ya hada a karar.

KU KARANTA: Wani Jigon APC a jihar Oyo ya rasu

Rahoton ya bayyana cewa wadanda su ka shigar da wannan karar, su na neman a fara shari’a da Ministan sufurin da kuma darekta janar na hukumar BPP.

Masu tuhumar jami’an gwamnatin, sun ce aikin Amaechi da Ahmadu ya ci karo da sashe na 58 (5) (a) na dokar bada kwangiloli na kasa na shekarar 2007.

Lauyoyin Insight Dynamic Resources su na neman kotu ta soke kwangilar da aka ba kamfanin Sin, Chinese Civil Engineering Construction Company.

Bayan haka, kamfanin na rokon kotu ta raba gardamar ko Ministan ya na da ikon ba CCECC takardar kwangila ta hannun shugaban hukumar BPP.

KU KARANTA: Kotu za ta yanke hukunci game da makomar sabon Sarkin Zazzau, Bamalli

Insight Dynamic Resources ya kalubalanci Amaechi da Ahmadu a Kotun Abuja
Buhari da Amaechi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Insight Dynamic Resources LTD na kukan cewa matakin da Ministan sufurin ya dauka, ya sa an toye hakkin sauran kamfanoni wajen neman kwangilar.

Lauyoyin da su ka tsaya wa Insight Dynamic Resources Limited a kotu, sun ce an saba sashe na 16 da 40 na dokar kwangila wajen bada wannan aiki na dogo.

A watan jita kun ji cewa Gwamnatin shugaba Buhari za ta nemo bashi nfam $11bn domin ayi aikin gina layin dogo tun daga Legas zuwa garin Kalaba.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi wannan magana lokacin da ya gana da wasu Igbo da kudu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel