An-jima Mutanen Zaria za su san ko za ayi nadin Sarki Ahmad Nuhu Bammalli

An-jima Mutanen Zaria za su san ko za ayi nadin Sarki Ahmad Nuhu Bammalli

- A ranar Juma’a ne kotun Dogarawa za ta saurari shari’ar nadin Sarkin Zazzau

- Iyan Zazzau ya na kalubalantar nadin da za ayi wa Amb. Ahmad Nuhu Bamalli

- Bashir Aminu ya roki kotu ta dakatar da bikin nadi da kuma mika sandar girma

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2020, babban kotun jihar Kaduna zai saurari shari’ar nadin sarkin Zazzau,.

Wannan kotu da ke zama a Zaria, jihar Kaduna, zai saurari karar da daya daga cikin Sarakan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ya shigar a gabansa.

A ranar Laraba, kotu ta saurari Lauyoyi masu shigar da kara da kuma masu kare wanda ake zargi.

KU KARANTA: Kotu ta sa ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau

Bayan an yi zama a ranar 4 ga watan Nuwamba, Alkali mai shari’a Kabir Dabo ya dage karar zuwa yau, ya ce a ranar Jum’a kotu za ta yanke hukunci.

Iyan Zazzau, Aminu ya roki Alkali ya bayyana shi a matsayin sabon Sarkin Zazzau, sannan ya yi fatali da nadin da gwamnati ta yi wa Ahmad Bamalli.

Lauyoyin Bashir Aminu sun kuma nemi alfarmar kotu a dakatar da bikin nadin sabon Sarkin Zazzau, sannan a hana mika wa Sarkin sandar girma.

Iya ya shigar da kara ne ta hannun Ustaz Yunus SAN a kotun da ke Dogarawa, Sabon Gari, Kaduna.

KU KARANTA: Hotunan sabon Sarkin Zazzau

An-jima Mutanen Zaria za su san ko za ayi nadin Sarki Ahmad Nuhu Bammalli
Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Idris Aliyu shi ne Lauyan da ya tsayawa gwamna da sakataren gwamnati da kwamishinan shari’ar Kaduna, ya kuma kare gwamnati a zaman da aka yi.

Daily Trust ta ce Lauyan da ya tsaya wa kwamishinar harkar masarautu shi ne Kenechukwu Azioyo. Lauyoyin sun roki ayi fatali da karar babban basaraken.

Za ku tuna tsohon hakimin sabon Garin ya na ikirarin masu nadin sarki sun mika wa gwamna Nasir El-Rufai sunansa a matsayin magajin Shehu Idris.

Mutane 10 ake kara a a wannan shari'a, daga ciki har da asir El-Rufai, babban Lauyan jihar Kaduna; Majalisar Sarakunan Kaduna; Majalisar Masarauta.

Sauran su ne: Wazirin Zazzau, Fagacin Zazzau, Makama Karamin Zazzau, Limamin Juma'an Zazzau, da Mai martaba Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng