Babban jigon APC Samuel Ojebode ya rasu a Oyo
- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa wani babban jigonta, Samuel Ojebode, a Oyo
- Ojebode, ya kasance Shugaban jam’iyyar a mazabar tarayya ta Oyo
- Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar sun nuna alhininsu kan mutuwar Ojebode
Abun bakin ciki da alhini ya samu jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayinda ta rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta, Samuel Ojebode.
Ojebode, wanda ya kasance jigon APC a jihar Oyo, ya rasu a ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamba, yana da shekaru 87 a duniya.
A wani sakon ta’aziyya, wani sanata daga jihar, Teslim Folarin, ya nuna bakin cikinsa.
KU KARANTA KUMA: Tsegumi da nishaɗi: Amaryar hadimin Buhari ta aikewa mijinta Bashir Ahmad zafafan kalamai
A wani jawabi daga Yakeeen Olaniyi a Ibadan, Folarin ya bayyana mutuwar a matsayin wani babban asara ga ahlin APC a Najeriya.
Folarin ya tuna cewa jigon na APC ya shirya taro na lumana mai cike da nasara ga mambobin jam’iyyar a mazabar Oyo ta tarayya.
Ya ce Ojebode ya kasance shugaba abun koyi, mai mutunci da kima.
A sakon ta’aziyyarsa, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Farfesa Adeolu Akande, Shugaban hukumar NCC, ya yi ta’aziyya ga iyalai, abokai da mambobin APC a jihar kan wannan rashi.
KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: ‘Yan bindiga sun sace malamin kwalejin Nuhu Bamalli da yara 2 a Zariya
A cewar Akande, Ojebode ya kasance dan siyasa na hakika kuma shugaba dab a a cika samun irinsa ba sannan cewa za a yi kewarsa.
A wani labari na daban, kwamishinan lafiya na jihar Benue, Dr Emmanuel Ikwulono, ya rasu, Nigerian Tribune ta ruwaito.
Ya maye gurbin Dr Sunday Ongbabo wanda ya yi murabus daga majalisar zartarwa ta jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng