Gwamnatin Buhari za ta nemi bashin $11bn don gina layin dogon Legas-Calabar
- Bayan shirin fara na Legas-Maiduguri, gwamnatin Buhari na shirin karbo sabon bashi domin gina layin dogo
- Ministan sufuri ya yi maganan ne ga yan'uwansa na kabilar Igbo da kudu maso kudu
Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, a rana Litinin, ya ce gwamnatin tarayya na shirin neman bashin dala bilyan 11 domin gina layin dogon Legas zuwa Calabar a jihar Cross River.
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin taron hira da kungiyar masanan yakin kudu maso yamma da kudu maso kudu watau South-East and South-South Professionals of Nigeria, SESSPN, a Legas, Vanguard ta ruwaito.
Kungiyar ta yi amfani da ziyarar da Ministan yayi zuwa Legas wajen tattaunawa da shi kan kalubalen da yankin ke fuskanta, musamman bangaren tsaro, wutan lantarki, da kuma romon demokradiyya a gwamnatin Buhari.
Yayinda yake magana kan dalilin da yasa har yanzu ba'a yi layin dogon jirgin kasa a yakin Igbo ba, yace: "Mun fara tsarin layin dogon Legas zuwa Calabar. Yanzu muna neman bashin $11billion domin gina layin dogon Legas zuwa Calabar."
DUBA NAN: Yanzu-yanzu: An saka dokar hana fita -ba dare, ba rana- a jihar Legas
Legit a baya ta ruwaito cewa majalisar zartarwa ta FEC ta amince da kwangilar titin dogo daga garin Fatakwal a kudu maso kudancin Najeriya zuwa Maiduguri, jihar Borno.
Gwamnatin tarayya za ta gyara wannan layin dogo, tare da gina sababin hanyoyi da na daukar kaya.
Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya na bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labarai a yau ranar Laraba. Da ya ke zantawa da ‘yan jarida bayan taron Ministocin tarayya a fadar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ce za a kashe Dala biliyan 3 wajen aikin.
Bayan haka gwamnatin tarayya ta amince da ginin tashar ruwa a Bonny a karkashin tsarin PPP inda gwamnati da ‘yan kasuwa za su yi karo-karon kudi.
KU KARANTA: An hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki musafaha da mace
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng