Rashin tsaro: Yadda aka yi awon gaba da mutane da-dama a hanyar Kaduna - Abuja

Rashin tsaro: Yadda aka yi awon gaba da mutane da-dama a hanyar Kaduna - Abuja

- ‘Yan bindiga sun yi barna a hanyar Kaduna zuwa Abuja a yammacin ranar Lahadi

- Miyagun sun kashe mutane akalla 15, sannan sun yi garkuwa da wasu Bayin Allah

- ‘Yan bindigan sun yi nasarar yin ta’adi ba tare da jami’an tsaro sun kawo doki ba

Akalla mutane 15 aka kashe, yayin da kuma aka yi gaba da wasu da-dama a lokacin da masu garkuwa da mutane su ka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ce wadannan miyagun ‘yan bindigan sun yi wannan aika-aika ne da kimanin karfe 5 na yamman ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba.

Lamarin ya auku ne a yankin Gidan Busa, wani kauye da ke kusa da garin Rijana, kilomita 133 kafin a shiga birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun hallaka mutane biyu a Jihar Kano

Kusan motoci 20 aka tsaida a wannan daji sa’ilin da ‘yan bindigan su ka yi ta’adin. A lokacin da aka auka wa matafiyan, babu wani jami’in tsaro a yankin.

Wadanda su ka samu labarin abin da ya faru sun bayyana cewa an kashe mutane 15 nan-take a wannan wuri, sannan an yi gaba da yara da mata cikin daji.

Majiyar ta ce masu garkuwa da mutanen sun zo ne dauke da miyagun makamai, su ka shiga buda wuta ga matafiyan da ke kan hanyar zuwa Abuja daga Kaduna.

Bayan tare titin, dole kowa ya tsaya, daga nan kuma aka shiga harbin duk wanda ya yi yunkurin ya tsere. Wata babbar mota mai cin mutum 18 aka fara tare wa.

KU KARANTA: An kama mutum 700 da makamai a Legas

Rashin tsaro: Yadda aka yi awon gaba da mutane da-dama a hanyar Kaduna - Abuja
Titin Abuja Hoto: www.stearsng.com
Asali: UGC

Wani mutum mai suna Mamman ya shaida wa ‘yan jarida yadda wata mota ta rika tangal-tangal bayan an harbi direbanta, daga nan aka dauke mutane zuwa jeji.

Da aka tuntubi ‘yan sanda, kakakin rundunar jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya bayyana cewa su na binciken lamarin, kuma za su yi jawabi daga baya.

A makon da ya gabata kun ji cewa wasu Miyagu sun shiga gidan shugaban majalisan jihar Adamawa, an tsere da mutane biyu ba tare da an san inda aka kai su ba.

'Yan sanda sun ce masu garkuwa da mutanem sun kashe Mai gadi, kafin su sace mutanen biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng