'Yan sanda sun kai samame maboyar masu laifi, sun kama mutane 720 da makamai a Legas

'Yan sanda sun kai samame maboyar masu laifi, sun kama mutane 720 da makamai a Legas

- Yan sanda sun kai samame maboyar masu aikata miyagu ayyuka a jihar Lagas

- A cikin haka, sun yi nasarar kama mutane 720 da makamai a fadin sassa 14 na jihar

- Hakan ya faru ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba

Rundunar yan sanda a jihar Lagas a ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamba, ta bayyana cewa ta kama mutane 720 mabuya daban-daban a jihar duk a cikin kokarin da ake na kakkabe laifuka.

Olumuyiwa Adejobi, kakakin yan sandan jihar, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa rundunar ta kai samamen ne a ranar Lahadi sannan ta kama masu laifin a yankuna 14.

An kuma samo makamai, layoyi, da miyagun kwayoyi.

'Yan sanda sun kai samame maboyar masu laifi, sun kama mutum 720 da makamai a Legas
'Yan sanda sun kai samame maboyar masu laifi, sun kama mutum 720 da makamai a Legas Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Mista Adejobi ya ce rundunar yan sandan jihar sun sake kaddamar da dabarunsu na yaki da masu laifi domin kakkabe miyagun laifuka a fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Babban jigon APC Samuel Ojebode ya rasu a Oyo

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin da aka karbo ana zaton an sato su ne a lokacin hare-haren da aka kai na fasa shaguna a yayin zanga-zangar EndSars.

Tuni dai kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu ya bayar da umarnin fara da bincike kan mutanen da aka kama domin gurfanar da su a gaban kotu, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Har ila yau, ya nemi wadanda aka yi wa sata a yayin zanga-zangar EndSars da su zo su duba kayayyakinsu da kuma shaidar cewa sune mamallakan kayan.

Ya kuma yaba wa 'yan sandan jihar bisa jajircewarsu wurin wannan samamen da suka kai.

KU KARANTA KUMA: Nasarun Minallah: Sojin Nigeria sun farmaki ISWAP, sun cafke masu haɗa makamin IEDs

Ya kuma bukaci jami'an tsaron da su kasance cikin ko ta kwana domin aiwatar da irin wannan samamen a nan gaba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa an shiga halin fargaba a jihar Kano bayan kisan wasu mutane biyu da ake zargin yan sandan da ke yaki da yan daba a jihar da aikatawa.

Yayinda ba a fitar da kowani jawabi da ke tabbatar da hakan daga mahukunta ba, an tattaro cewa an harbe matasan ne a unguwar Sharada lokacin da sashin yaki da yan daba suka ziyarci yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng